Sheikh Dahiru Usman Bauchi OFR Ya Jagoranci Zaman A Fadar Shugaban Kasan Najeriya.

Maulanmu Sheikh Dahiru Bauchi RA.

 

Ya Jagoranci Zaman A Fadar Shugaban Kasa Tare Da Jagororin Addinin Musulunci Na Kowanne Bangare.

 

Shahararren malamin Addinin Musulunci Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA ya jagoranci shugabannin addinin Musulunci ganawa ta musamman a fadar shugaban ƙasar Nigeria domin tattaunawa kan matsalolin da Nigeria ke ciki a halin yanzu kan shanin Addini da ma sauran matsalolin na ƙasar a ranar 9-8-2023.

 

Zaman ya gudana ne tare da shugaban ƙasar Bola Ahmad Tunibu da sauran membobin zartarwa na kasa da jagororin ƙungiyoyin addinai na Ɗarikƙa, Qadiriyya, da na Izala kan yadda za’a shawo matsalolin rikicin addini da neman shawari a addinance wajen magance sauran abubuwan da ke samun Nigeria waɗan da ba’a bayya na ba

 

Zaman yayi nasara domin an cimma kyawawan matsaya kan hanyoyin da za’a bi domin magance dukkan matsalolin.

 

Allah ya bamu zaman lafiya a Najeriya. Amiin

 

Daga: MUHAMMAD ALMARKAZY

Share

Back to top button