Sheikh Dr, Usman Nuhu Sharubutu RA Zai Bude Katafaren Masallacin Juma’a A Ghana.

ZA’A BUDE SABON KATAFAREN MASALLACIN JUMA’A WANDA BABU IRIN SA A GHANA.

 

Babban limamin kasar Ghana kuma malamin Musulunci a duniya kuma shugaban majalisar koli ta addinin Islama a kasar Ghana Sheikh Dr, Usman Nuhu Sharubutu (RA) ya gina babban katafaren masallacin juma’a wanda babu irin sa a duk fadin kasar tare da makarantar haddar Alkur’ani mai girma (Tahfeezul Qur’an).

 

Za’a bude sabon masallacin sa da aka gina da makarantar haddar Alkur’ani (Tahfeezul Qur’an) kamar haka;

 

* Rana: Juma’a 5 ga Augusta, 2022

* Lokaci: 10:00 na safe.

* Wuri: Ablekuma Joma, Accra Ghana.

 

Muna addu’an Allah ya kara tsawaita rayuwar IMAM, Allah ya kara lafiya da nisan kwana, ya bamu albarkacin su. Amiin

 

Babangida A Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button