Sheikh Farfesa Ibrahim Ahmad Maqari Limamin Abuja Ya Cika Shekara 47 A Duniya.
SHEIKH IBRAHIM MAQARI @47
Kwararren Farfesa Malamin Addinin Islama A Duniya Babban Limamin Masallacin Abuja Sheikh Ibrahim Ahmad Maqari Hafizafullah Ya Cika Shekara Arba’in Da Bakwai (47) A Duniya.
Farfesa Sheikh Ibrahim Maqari Babban Malamin Islama, Jigo A Darikar Tijjaniyya Kwararren Farfesa Wanda Ya Wallafa Littatafai A Fannin Musulunci Da Zamantakewa A Islama, Farfesa Maqari Ya Haddace Littafai Kamar Alkur’ani Mai Girma, Sahihul Muslim, Sahihul Bukhari, Da Dubban Littafai Masu Tarin Yawa.
Farfesa Ibrahim Gogagge Ne A Ilimin Sanin Halayan Manzon Allah SAW Da Bayin Allah Waliyai, Ya Kasance Masanin Ilimin Fikhu, Nahwu, Balaga, Sira, Tawhid, Sauran Ilmomin Addinin Islama.
Muna Addu’an Allah Ya Kara Wa Maulana Farfesa Ibrahim Maqari Lafiya Da Daukaka, Ya Kare Shi Daga Sharrin Makiya. Amiin
Babangida Alhaji Maina
Founder Tijjaniyya Media News
National Director Fityanu Media