Sheikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi, Ya Halarci Wa’azin Da Kungiyar Izala Ta Gudanar A Garin Misau, Jihar Bauchi

Sheikh Ibrahim Dahiru Usman Bauchi, Ya Halarci Wa’azin Da Kungiyar Izala Ta Gudanar Jiya Da Dare A Garin Misau Dake Jihar Bauchi

 

Daga Comr Abba Sani Pantami

 

Shugaban kungiyar na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau ne ya jagoranci wa’azin tare sakataren kungiyar Izala na kasa Sheikh Dr. Muhammad Kabiru Haruna Gombe da sauran manyan jiga-jigan kungiyar Izala.

 

Sheikh Ibrahim Dahiru usman Bauchi ya wakilci sarkin musulmi ne a wajen wa’azin, an gudanar da wa’azin ne daren Asabar a kofar mai martaba sarkin Misau dake jihar BAUCHI.

 

Na tabbata dubbannin musulmai ne za suyi farin cikin ganin ana samun hadin kai a tsakanin jagororin bangarori na musulmi a Najeriya.

 

Allah ya taimaki shugabannin mu ya kara musu hadin kai, ya kara dorasu akan daidai. Amiin

Share

Back to top button