Sheikh Ibrahim Inyass RA Babban Malamin Musulunci Wanda Duniyar Ilmi Ta Sallama Masa.

SU WAYE MAKIYA DA MAHASSADANSA DA YA NEMI TSARIN ALLAH DAGA KAIDINSU A CIKIN LITTAFINSA NA DIWANI.

 

Daga abinda R/Lemo ya kuskure..!

 

A zamanin rayuwarsa, Maulanmu Sheikh Ibrahim Inyass (R.T.A) yana daga cikin Maluman da suka yi fito-na-fito da turawan Mulkin mallaka akan nemawa kasashen Africa yancin kai, yayi tarayya da gwarazan da suka sadaukar da rayuwarsu akan wannan layi, tare kuma da rubuta wasiku da litattafai, tattaunawa da manyan gidajen jaridun Duniya akan haka, cikin litattafan da ya rubuta domin yakar mulkin mallaka da turawan yammacin Duniya ke yiwa kasashen Africa akwai shahararriyar littafinsa mai suna إفريقيا إلى الإفريقيين wato Africa zuwa ga mutanen Africa.

 

Wannan jarumta tasa, sai ta zamo wata aba da ta jawo masa bakin jini matuka a idanun turawan mulkin Mallaka na Duniya, sai ya zamo suna ta kirdado da tsare-tsaren yadda zasu bullo masa su yake shi, hakanan suka fuskace shi da cutarwa nau’i nau’i.

 

Ganin bai da wata madogara, majibanta da makoma da ya fice ALLAH, shi ne yake tawassali da MANZON ALLAH (S.A.W) cikin littafinsa na diwani yana mai jerin gwanon Addu’oi akan ALLAH ya kareshi, tare da bashi rinjaye akan sharrin makiyansa wadanda sune wadannan turawa da Yahudawa da suka sanya shi gaba, kuma ko a siffa ta Waliyyan ALLAH idan suka roki ALLAH to zai amsa musu, idan kuma suka nemi jibanci gareshi zai basu mafaka.

وإن سألني أعطيته، ولئن استعاذني لأعيذنه

 

Sai ya zamto a wasu baitocin yana godewa ALLAH da yadda ya bashi kariya daga makircin makiyansa (Turawa da Yahudawa) da suka nufeshi da cutarwa kala-kala.

 

Annabawan ALLAH su kan roki ALLAH akan basu kariya, ko nasara akan Azzaluman Zamaninsu, wasu kam cikinsu har Aduo’i sukayi akan ALLAH ya hallaka Al’ummarsu ko a yayin da suka ki karbar sako, kuma suka wai-waice su da cutarwa.

 

Saboda haka, duk inda akaji Shehu na ambaton Makiya ko Mahassada, to bai nufin Musulmi wanda ya saba da shi a fahimta, bal yana nufin wadannan Turawan da su ka sanya shi a gaba da nufin cutarwa.

 

Muna rokon ALLAH ya ganar da Rijiyar Lemo, ya fahimci alkairin dake tattare da Rijiyar Zuma ko ya zamo cikin masu rabauta. Amiin

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua.

Share

Back to top button