Sheikh Ibrahim Inyass Yana Da Almajirai Sama Da Miliyan Takawas 8 Tun Shekara Sittin Da Suka Shige.

Shehu Ibrahim Inyass Ne Kadai Malamin Da Ya Tara Almajirai Sama Da Miliyan 8 A Zamanin Rayuwansa A Duniyar Musulunci

 

Jaridar karshen sati ta kasar Misra ta ruwaito ta hannun ma’aikacinta mai suna Jamilu Arif a ranar 11 ga watan Yuni Shekarar 1961 cewa;

 

” JAGORAN ADDININ MUSULUNCI MAI SUNA SHEIKH IBRAHIM NIASS, TABBAS SHINE SHEKHUL ISLAM, A BINCIKEN DA MUKA YI YANA DA ALMAJIRAI FIYE DA MILYAN 8 A IYA AFRICA ”

 

Dan uwa, Idan kayi nazari daga ranar da jaridar ta fita, zuwa yau shekara 61 kenan. Me zai hana kayi naka binciken a yau, domin gano aqalla almajirai milyon nawa SHEHUN ke dasu a yanxu ?

 

Ga jahili, yawan almajiran ne zasu dimautar da shi, amma mai ilimi abinda zai fara bincikawa shine su waye almajiran.

 

Nasan yawan nasu zai iya gigita ko ma waye, duba da ba wanda ya taba kafa wannan tarihin a Duniyar Islama a lokacin rayuwansa

 

Haka sahihancin almajiran, domin a Gaskiyance babu kama ko irin su.

 

Da zaka dauki daya daga cikin almajiran domin bayyana sahihancin sa, to da rayuwar da ta rage maka, baza ta isheka kai matuqa wajan gamsarwa ba. To ina kuma ga shi Malamin ?

 

YA ALLAH DUK RINTSI, HALIN RASHI DA SAMU, HALIN QUNCI DA WALWALA, HALIN MATSI DA YALWA, HALIN LAFIYA DA CUTA, HALIN KIMA DA QASQANCI, HALIN EH DA A’A, HALIN HA MAZA HA MATA.. ALLAH KA BARMU A CIKIN TAWAGAR MASOYA SHEHU IBRAHIM RTA MASOYIN MANZON ALLAH S A W. Amin

Share

Back to top button