Sheikh Ibrahim Maqari Ya Bayyana Matsayar Sa Bayan Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa 2023 A Najeriya.

DALILAN DA SUKA HAIFAR DA WANNAN TUNANIN (A FAHIMTATA).

 

1- Zamowarsa Limami a babban Masallacin kasa, hakkinsane ya zamo mai yin kira akan duk abinda zai tabbatar da dorewar Nigeria a matsayin kasa daya, al’umma daya, daga barin duk abinda zai haifar da wariya, tsangwama ko kuma cin fuskar ga wasu al’umma, ta hanyar aje dukkan banbance-banbance.

 

2- Wannan dalilin yasanya yayi iya kokarinsa matuka cikin karatuttukansa yana mai kira akan a kasa irin ta Nigeria da take Secular State, a zabi chanchanta daga barin duba bambancin Addini, Jam’iyya ko kuma bangaranci, shine Malami guda cikin Malamai da na sani wanda bai dauki bangare ba a siyasa baldai yana nun ko da Kristane yafi Musulmi chanchanta, to a zabi Kristan ta hanyar barin Musulmin.

 

3- Ko da yake wasu bangaren Yan Siyasa, sun shigo da Addini cikin harkalarsu, ta hanyar Muslim-Muslim Ticket, a lokacin da ake ganin idan Musulmi ya fito daga Arewa, to Mataimakinsa zai zamo wanda ba Musulmi ba daga kudu a bisa ga Al’ada, sai aka samu wasu daga Maluman Addini suka fito karara suka nuna kyamar Kristoci a zahiri, mai yiwuwa su kuma sai hakan ya basu haske akan cewa bara suma su hade wuri guda su zabi nasu.

 

4- Kaga kenan hakan darasine ga Maulana Prof. Ibrahim Maqari da yake ta kira akan Tolerance, a nesanci bangaranci, ya fahimci cewa “wadanda yake yi dominsu duk basu duba hakan face su kawai na su suka sani, kuma shi suka sanya a gaba”.

 

A KARSHE DAI SHIMA MAI YIWUWA YANA GAB DA SAUYA MATSAYA ZUWA GA KIRA GA A ZABI MUSULMI MAI NAGARTAR HALAYE A ZABUKA MASU ZUWA.

 

ALLAH SHI KYAUTA. AMIIN YAA ALLAH

 

Daga: Muhammad Usman Gashua

Share

Back to top button