Sheikh Ibrahim Musaddad Jos Ya Cika Shekaru Ashirin (20), Da Komawar Sa Ga Allah.

Sheikh Ibrahim Musaddad Jos Ya Cika Shekaru Ashirin (20), Da Komawar Sa Ga Allah.

 

A rana mai kamar ta yau 24 ga watan Zul-Hijjah, shekaru Ashirin daidai da suka wuce ranar Lahadi bayan Sallar La’asar, Maulanmu Sheikh Ibrahim Musaddad Jos, yayi wafati bayan ya kammala Majlisi ga masu ziyarar sa, an tafi an barshi yana cikin Lazuminsa, sai zuwa akayi aka zare carbin a hannunsa.

 

Shehi ya rayu cikin jinya sosai, amma idan mutum yaji labarin bautarsa cikin Allah zai iya zaton ba a wannan zamanin aka yi shi ba. Kyan zuciyar sa da nufin kowa da Alkairi yasa har Kiristoci da ke bauta a unguwar sa kanzo gaida shi ko kuma suzo sulhu in sun samu ɓaraka.

 

Ƙarƙashin makaranta da ya assasa wacce ke gidan shi, an samu dubban wanda suka sauke Alqur’ani da wanda suka haddace shi, kuma galibin ƴaƴan da Allah ya azurtashi dasu kusan talatin da ɗaya wanda ya bari a duniya Mahaddatan Alqur’ani ne.

 

Indai Shehi baya Wuridi to yana yiwa baƙi ko masu Ziyara Majalisi, in kuwa ba haka ba to Karatu yake, wannan shine aikin har aka koma ga Allah.

 

Allah ya ƙara bamu albarkacin su, ya kuma tabbatar damu akan tafarkin su da koyarwar su. Amiin

 

Daga: Sabo Ibrahim Hassan

Share

Back to top button