Sheikh Imam Mansur Kaduna Yace: Duk kungiyoyi da kuke gani ake bude wa da sunan Tijjaniyya duk yaudara ne kawai.

DAGA SHEIKH MANSUR IMAM KADUNA.

 

” Duk kungiyoyi da kuke gani ake bude wa da sunan Tijjaniyya duk yaudara ne kawai, ana amfani da yawan ku ne a sayar da ku a wajen yan siyasa a zagaya a karbi kudade ku kuma a bar ku kuna ta Inyass Inyass kuna Zikiri a rana”

 

“Su kuma da sun amshi Kudi sai su tafi London ko Umra”

 

“Idan sun je Umrar ma ba Ibada suke yi ba hotel suke kamawa suyi ta Chin Nama har su dawo”

 

“Ta inda zaka tabbatar da hakan idan za ayi taron ba a karanta tarihin Shehu Tijjani ko Na Shehu Ibrahim, ana haduwa yabon yan Siyasa kawai za ayi ta yi”

 

” Amma maganar nan kwakwata basa so ana yin ta sai kuma muda muke yin sun gagara daukar Mataki”

 

” Saboda haka idan zaku hankalta Ku hankalta ku bi Allah ku Rabu da Kungiyoyin nan”

 

Yayi bayanin haka a Karatun Littafin Hikamu Ada iyya, Darasi na 12.

 

Allah ya karawa Maulana Sheikh Imam Mansur Kaduna lafiya da daukaka. Amiin

Share

Back to top button