Sheikh Imam Munir Adam Koza, Baka Fadi Komai Ba Face Gaskiya.

ALLAH YA SAKA DA ALKAIRI.

 

Sam-sam babu bukatar turo da kowanne guda daya daga cikin Manzanni zuwa ga al’ummu da suka gabata, da sakonnin da suke fayyace dai-dai da kuskure, gaskiya da karya, shiriya da kuma bata, cikin tsari da dokokin da ubangijin bayi yakeso bayinsa su rayu akai ta hanyar saukar da litattafai mabambanta, idan da ace kowa abinda ya kimtsa a tunaninsa, na ra’ayinsa da kuma sha’awowinsa shine Addini a gareshi.

 

Amma lallai muddin mun yarda mu Musulmine, kuma munyar da akwai MANZON da aka aikoshi da tsarin rayuwar da ALLAH yakeso mu rayu akai a wannan zamanin, kuma mun aminta mu al’ummarsane kuma mun yarda dukkanin jagororin da muke tutiya dasu basu kasance masu sabawa abinda yazo dashi ba, to bin wannan tsarin rayuwar da MANZO (S.A.W) yazo dashi shine dai-dai kuma shine mafifici karbabbe a wajen ALLAH, duk wani tsarin rayuwa sa6anin wannan lalataccene, gurbataccene, sannan kuma bai kasance abin bi ga wadanda suka kasance suna rayuwa bisa neman dai-daito da dacewa da shiriya ba.

 

Babu shakka Sheikh Imam Munir Adam Khoza, baka fadi komai ba face gaskiya, kuma lallai komawa zuwa ga abinda magabatan da muke intisabi dasu, shine gaskiyar tafarki na shiriya, sabanin hakan babu inda zai kaimu, face muna tunanin mu mabiyansune masoyansu, amma a hakika mu masu saba musu ne, sannan makiya ga abinda suka dora mu akai.

 

Lallaine dama wannan abune tabbatacce da ya wanzu a tarihin Duniya, a duk inda gaskiya ta gifto ta motsa to takan nufi inda alkairi ya dosa, kuma a duk inda Alkairi ya wanzu to sharri kan biyoshi a sukwane domin ya kishiyancesa.

 

FATANMU ALLAH YA TABBATAR DA MAGASKATA AKAN GASKIYARSU, YA SHIRYI MASU HIDIMA GA AKASINTA A DUK INDA SUKE. Alhamdulillah

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua

Back to top button