Sheikh Inyass Ne Ya Kawo Kablu Nijeriya, Yayin Da ‘Yan Shi’a Suka Kawo Hijabi – Sayyadi Abul Fath Sani Attijaniy.

Sheikh Inyass Ne Ya Kawo Kablu Nijeriya, Yayin da ‘yan Shi’a Suka Kawo Hijabi – Sayyadi Abul Fath Sani Attijaniy.

 

Daga Mujahid Umar D Giwa.

 

Shaikh Abulfathi Sani Attijjani wanda akafi sani da Zakin Faida ya bayyana cewa shehunan daria ne suka fara kawo Sunnar Kablu rike hanu yayin sallah dan haka yanzu duk wanda ya rike hanu a sallah to shehunan darikar suna da ladan karantar da wannan sunnah din.

 

A gefe guda kuma ya kara da cewa mabiya shi’ah ne suka fara kawo sunnar sanya hijabi a Najeriya, yace da baya ba’asan hijabi ba sai dai wani mayafi sai ‘yan shi’ah suka shigo suka koyar da sanya hijabin.

 

A karshe ya kalubanci ‘yan Izala da su fito su nuna Sunna daya da suka taba kawo wa Najeriya.

 

Sayyadi Abul Fath Zakin Faidah wanda yayi Shura a bangaren kalubalantar yan izala da wahabiya yanda suka yin addini Musulunci tare da raddi mai zafi ga Ja’afar da Albani Zaria.

 

Allah ya karawa Sayyadi Abul Fath Sani Attijany lafiya. Amiiiin

Share

Back to top button