Sheikh Karibullah Ya Jiƙa Gàshìn Manzon A Allah A Ruwa Domin Shayar Da Al’umma.

Sheikh Karibullah Ya Jiƙa Gàshìn Manzon A Allah A Ruwa Domin Shayar Da Al’umma.

 

Yadda aka hangi Shugaban Ɗariƙar Ƙadiriyya na ƙasa wato Sheikh Karibullah Nasiru Kabara Kano, ya fito da silin gàshìn Manzon Allah (SAW) a cikin wani abu da aka killace mai cike da girmamawa, kamar yadda babban shehin ya yi ikirarin haka.

 

Hakan ya ƙara jan hankali al’umma tare da dubban mabiya, a bisani an hangi babban malamin ya fito da silin na gàshìn gaban mabiyansa ya na tsomawa a cikin ruwa domin shayar da al’umma, neman tabarraki kamar yadda aka saba gudanar da wannan taron duk shekara.

 

Idan ba ku manta ba a bara ne babban malamin ya bayyanama duniya hakan na mallakan gàshìn Manzon Allah (SAW) a cewarsa; da hakan ya ja hankalin Al’ummar Najeriya da ma duniya baki ɗaya a kafofin sada zumunta.

 

Allah ya bamu albarkan gashin Manzon Allah SAW duniya da lahira. Amiin

Share

Back to top button