Sheikh Mijinyawa Ya Kasance Babban Waliyi, Sufi A Darikar Tijjaniyya A Duniya Baki Daya.

Sheikh Mijinyawa cikakken dan jihar Kano ne, an haife shi a shekara 1313 kafin zuwan turawa kasar kano da shekara takwas (8).

 

Babban Malamin yayi rubuce-rubuce da dama a bangaren addinin Musulunci kamar Fiqhu, Nahwu, Tafsir, Lunga da sauran su. ya bada gudumawa sosai don yada addinin Musulunci a yammacin Africa tare da amfanar da dukkan al’umma wurin zamantakewa, mu’amala da kuma rayuwa.

 

Tarihin ya tabbatar da cewa lokacin da Sharif Muhammad Alami Yazo Najeriya a shekara ta 1923, Malam Mijinyawa shine yake masa tarjama zuwa yaren Hausa tare da sakatare.

 

Sheikh Abubukar Mijinyawa ya rasu a ranar 4/03/2/1946 wanda yayi dai-dai da 11/03/1366 an masa makwancin sa a jihar kano.

 

Muna addu’an Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa ya jaddada rahma a gare shi, Allah ya kara masa kusanci da Manzon Allah SAW. Amiin Yaa ALLAH

 

Daga: Babangida A. Maina

Founder Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button