Sheikh Muhammad Dan Almajiri Ya Hana Almajiransa Bara, Kuma Shine Mutum Na Farko Daya Fara Tsarin Islamiyya a Nigeria.

DOKAR HANA BARA A NIGERIA.

 

Tun kafin Abawa Nigeria ƴancin kai

Maulana Sheikh Muhammad Dan Almajiri yahana Almajiransa bara, kuma shi ne mutum na farko daya fara tsarin islamiyya a Nigeria.

 

Shehin yace bai kamata mai naiman har dar Alqur’ani mai girma yana cin sauran Abincin ko wane irin mutum ba zai yi kyau ya rinka cin tsar ka kakken Abinci ko Abinsha.

 

Hakan ne yasa maulana shehu dan Almajiri daga Unguwa Fagge yafita wajen gari a unguwar Rijiyar Lemo kan titin katsina rood kano ya sayi gonaki yagina masallaci da makaranta sauran fulotan ya rabawa Almajiransa masu rauni, sanan ya radawa wannan gari da suna DAIBA wato sunan garin da Aka haifi Shehu Ibrahim Niass domin naiman Albarka.

 

Shehu dan Almajiri har shehu Malam Tijjani zangon bare bari ya ginawa gida a DAIBA da zummar ya taso daga zangon bare bari ƴen mota ya dawo wannan unguwa.

 

A cigaba da kafa wannan unguwa DAIBA watarana akan han yarsa ta komawa Fagge daga Daiba sukayi Hadari a dai dai kurna masallaci shida daya daga manyan hadimansa Sheik Haruna Rasheed Allah yayiwa shehu Dan Almajiri rasuwa Allah ya sakamusu da mafificin Alkhairi.

 

Abin lura shine Allah ya karbi wannan Aikin da shehin yayi yunkuri domin unguwar ta tafi yanda shehin ya tsarata har yanzu Almajiran makarantar sa basayin bara takai da babu inda ake hardace Alqur’ani mai girma kamar a wannan makaranta ta DAIBA kuma tana da dubban rassa a gida Nigeria da wajenta cikin wannan tsari na har dace Alqur’ani da sauran ilimmai ba tare da baraba.

 

Muna kira ga Gwamnatin Tarayya dana jahohi da su naimi shawarar khalifan Shehu Muhammad dan Almajiri da sauran masana domin naiman shawar warin da za’abi dan kawo karshen bara da dai daita karatun Alqur’ani mai girma cikin sauki ba tare da An batawa kowaba.

 

Marubuci Hafizu Aminu Daiba

Share

Back to top button