Sheikh Prof Ibrahim Ahmad Maqari Hafizafullah Shine Babban Limamin Masallacin Abuja.
MAKIRCI DA HASSADAR KU , BAZA SU ZAMO KOMAI BA, FACE KARIN DAUKAKA DA DARAJA A GARESHI.
….. Rabu da su!, tsammaninsu rashin abin fadane ya san ya ya zamo mai yawan juriya da hakuri, tare da kawar da idanu daga barin mayar da martani akan wawta da kuma gidadancin maridai, inda kowanne shawaragin ya taso da niyar neman shuhura, ya rasa wajen zubda kwamacalarsa sai ya zubda agareshi, to wallahi ku shiga taitayinku (Wahabiyawa).
Ka da ku yi tsammanin kun fi mu wata zarrah, ko kuma wani salo da zaku iya amfani dashi wajen muzanta mana jagorori da bazamu iya amfani da wanda ya fishi wajen muzanta na ku ba, illa dai tarbiyyar da akayi mana da taku ce ta bambanta.
Limancinsa ya tsole muku idanu, saboda wurin da yake kai da ace wasun ku ne a wajen, to da sun samu masana’antar da zasuyi amfani da ita wajen wankar masu mulki da ‘yan siyasa domin tara abin Duniya, amma kasancewarsa mai gudun Duniya, da fede gaskiya cikin duk abinda ya wakana, tare da aikata gaskiyar da ke tona asirin ha’incinku cikin addini, sai hakan ke hassalaku, tare da bibiyar hanyoyi mabambanta na shirya manakisa da makirce-makirce gareshi.
Wallahi ba za ku taba yin galaba ba, domin mutane wadanda ALLAH ya azurta da irin dabi’unsa, da kuma ayyukansa na ciyar da al’umma gaba, dabi’u na tausayi da kuma jinkai ga bayin ALLAH, ba za su taba tozarta ba, ko da an jarabci wawaye da tsananin kiyayya a garesu da kuma makirci.
Duk da kasancer shi mai hakurine, tare da hakurtar da dukkanin masoyansa akan kada suke mayar da martani cikin ababen da ake kirkira ana jingina nasa na cin mutumci da kuma kazafi, to amma idan muka gaza tsaida birkin soyayya muka hau kanku da irin kalmomin da kuka fi iya ganewa, to lallai zaku fahimci mun fi ku zarra ta kowacce fuska.
KU NUTSU KUSAN ME KUKEYI.
IDAN KUNNE YAJI….!
Daga: Muhammadu Usman Gashua