Sheikh Sharif Ahmad Aliyu Abulfathi Babban Malamin Musulunci Kuma Jigo A Darikar Tijjaniyya.

ANNABI MUHAMMADU(S.A.W);

 

Tsabar KusancinSA (S.A.W); Har Sai Da ALLAH(S.W.T) Ya Mayar Da Yiwa ANNABI (S.A.W) Salati ‘Daya Daga Siffofinsa, Sannan Ya Arawa ANNABIN Duka Sunayensa In Ka Cire ALLAHU. Bai Tsaya Nan Ba Sai Da Ya Mayar Da AikinSA (S.A.W) Ya Zam AikinSA (ALLAH(S.W.T).

 

*. Mu Sa Lura Da Tafakkurin Waɗannan:

 

In Aiki Don ANNABI(S.A.W) Shirka Ne To Yaya ALLAH Ya Ce:

 

a. من يطع الرسول فقد عطاع الله

 

WANDA YA YIWA MANZO (S.A.W) ƊA’A HAƘIƘA YA YIWA ALLAH ƊA’A.

 

b. Ya ANNABI(S.A.W) Ya Ce:

 

فمن كانت هجرته الي الله ورسوله فهجرته الي الله ورسوله

ومن كانت هجرته لدنيا يسيبها او امرءة ينكحها فهجرته الي ما هاجر اليه.

 

“Wanda Yayi Hijira Domin ALLAH DA MANZONSA(S.A.W) Sakamakon Hijirarsa Yana Ga ALLAH DA MANZONSA(S.A.W), Wanda Yayi Hijira Don Duniya, Zai Same Ta, Ko Don Wata Mace Da Zai Aura To Sakamakon Hijirarsa Yana Ga Abin Da Yayi Hijira Dominsa”.

 

KU KALLI SIYAƘIN DA KYAU; ANNABI (S.A.W) YA HAƊA SUNAN ALLAH DA NASA A CIKIN AIKI, KARƁARSA DA SAKAMAKONSA.

 

Sannan Wai Aka Yi Aiki Don Duniya Ko Mace Ma ANNABI(S.A.W) Bai Ce An Yi Shirka Ba Sai Ku??? Kun Fi ANNABI(S.A.W) Tauhidi Ne??? Shi ANNABI(S.A.W) Kawai Nuni Yayi Da Cewa; Babu Lada, Bai Ce Shirka Ba.

 

To Wannan Fa Tarkacen Duniya Kenan.

 

c. Akwai Hadisi Sahihi a Sahihul Bukhari Wanda Wani Bayahude Ya Bi ANNABI (S.A.W) Yaƙi Kuma Ba Don Ya Musulunta Ba, Kawai Don ANNABIN (S.A.W), Har Sai Da Ya Shelantawa Jama’arsu Sannan Ya Tabbatar Da Cewa; Don Yana Son ANNABI(S.A.W) Zai Je Yaƙin Ba Don Ya Musulunta Ba.

 

Har IMAMUL BUKHARI Ya ‘Kara Da “WALAM YUSALLI SALATAN…..” – Ma’ana; Bai Taɓa Aikata ‘Daya Daga Shika-Shikai Ba. An Kashe Shi a Wurin Yaƙin Kuma MANZO(S.A.W) Yayi Shaidarsa Da Cewa;”HUWA KHAIRUL YAHUDI”.

 

ALLAH Ya ‘Kara Tsare Mana Imaninmu, Ya ‘Kara Mana Ganin Girma Da Qadarin ANNABINMU (S.A.W) Ameeeeen.

Share

Back to top button