Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al Hussaini Shugaban Majalisar Malamai Na Najeriya Baki Daya.

Wani Ya Tambayeni Kamar Haka!

 

Dan Allah Malam Imam Anas, me yasa ban cika ganin abubuwan Maulana ba, kuma mutanen Nigeria basu cika yaɗa abubuwan saba ina nufin Maulana Sheik Shariff Ibrahim Saleh Al-Husain Maiduguri kamar sauran malamai.

 

Amasar Dana Bashi.

 

Shi malamin malamai ne kuma malamin duniya ne, ba malamin Nigeria bane, a majalisar malamai ta duniya a yanzu haka shine mutum mai daraja ta biyu a majalisar malamai ta Azhar shine mai daraja ta biyu, a majalisar malamai ta Nigeria, shine mai daraja ta ɗaya.

 

Duniya ce tasan waye shi amma yayi ma Nigeria girma shi yasa lamuransa sai dai ka gani ana yaɗawa a duniyance ba a Nigerian ce ba.

 

Ba kaga gidauniyar daya haɗa ba, ta buɗe cibiyar bincike ta ilimi mafi girma a Africa ba, wacce akeyi anan Nigeria, babu wata ƙasa ta Musulunci da bata bada gudunmawa ba, tare da manyan attajirai na duniya dana Nigeria, kusan Trillion ya haɗa a lokaci ɗaya.

 

Allah ya ƙara ma malam lafiya, tare da jinkiri mai amfani haƙiƙa a wannan ƙarnin wallahi babu kamarsa. Amiin Yaa ALLAH.

 

Daga: Malam Imam Anas

Share

Back to top button