Shekara 48 Da Wafatin Sheikh Muhammadu Ngibirima Nguru RA A Dake Nguru Jihar Yobe.

Yau Shekaru Arba’in Da Takwas (48) Da Watafin Sheikh Muhammadu Ngibirima Nguru

 

A irin wannan rana ta 19/02/1975, Allah ya karbi rayuwar sanannen malamin Musulunci wanda ya bawa duniyar darika kariya Sheikh Muhammadu Ngibirima Nguru dake garin Guru dake jihar Yobe.

 

Sheikh Muhammadu Ngibirima Zulma Arif shahararren malamin Musulunci ne, kuma jigo a darikar Tijjaniyya wanda ya bada gagarumar gudumawa wurin daukaka Addinin Musulunci tare da zamantakewa a yankin Africa.

 

Shekaru Arba’in da takwas (48) kenan da rasuwan shehin malamin a lissafin miladiya. Ta 19/02/1975

 

Allah ya jikan sa da rahma ya gafarta masa, muna sddu’an Allah ya karbi bakwancin sa. Amiiiin Yaa Allah

 

Babangida A. Maina

Tijjaniyya Media News

Share

Back to top button