Shekara 7 Nayi Ina Rubuta Waƙar Da Nayi Wa Manzon Allah. Inji Alan Waƙa

Shekara 7 na yi ina rubuta waƙar da nai wa Manzon Allah — Alan Waƙa

 

Shahararren Mawakin Hausa wanda yake kira Alan Waka ya bayyana cewa shekara bakwai (7) yayi naya rubuta waƙar yabon Manzon Allah SAW. Inji Alan Waka.

 

“Shekaru 7 Na Yi Ina Rubuta Waƙar Da Na Yi Wa Manzon Allah S A W”, Cewar Alan Waƙa.

 

Shahararren mawakin Hausar nan, Aminuddeen Ladan Abubakar ‘, wanda aka fi sani da Alan Waƙa, ya ce ya dauki kimanin shekaru 7 ya na rubuta waƙar da ya yiwa fiyayyen halitta, Manzon Allah (S.AW), wacce ya sanyawa suna “Muhammadu miftahul futuhati linzamin rayuwata”.

 

Yace ya kwashe shekarun ne kafin ya kammala rubuta waƙar saboda sai da ya gudanar da bincike mai zurfi, inda ya ƙara da cewa waƙar ta shafi tarihin rayuwar Annabi Muhammad (S A W) tun daga haihuwa har zuwa wafatin sa.

 

“Irin wannan babban aiki yana matukar bukatar bincike na tarihi da kuma irin kalmomin da za’a yi su akan Fiyayyen Halitta, don gudun zarmewa”. Inji Alan waka

 

Hakazalika yace ita waka “Mufitahul futuhati” littafi ne ya mayar da shi waka saboda mutane da dama su amfana, inda ya ƙara da cewa babu shakka mutane sun ji dadin wakar “kuma nima Ina alfahari da ita.”

 

Ya ce mafiyawan wakokinsa yana gina sune kan Ilimi kuma yana gudanar da bincike kafin yayi kowacce irin waka, inda ya ce “domin yin hakan shi yake bani damar fadin abun da yake dai-dai akan duk wanda zai yiwa waka.” inji Aminu Alan Waƙa

 

ALLAH ya kara basira da hazaqa, Allah ya tabbatar damu cikin soyayyan Manzon Allah SAW. Amiin

 

 

Share

Back to top button