Shekarunsa Suna Raguwa Amma Baya Tuhumar Kansa Akan Haka.

A KOWACE SAFIYA DAN ADAM YANA HADUWA DA BALA’I GUDA UKKU

 

*Na farko 1*

*Shekarunsa suna raguwa amma baya tuhumar kansa akan haka.*

*Idan kudinsa ya ragu xai tuhuma bayan kudi yana dawowa amma shekaru basa dawowa.*

 

*Na biyu 2*

*kullum yana cin arxikin Allah in halal yaci xa’a tambaye shi in haram ne xa’ayi masa axaba akai bai san karshen hisabin mai xai kasanceba.*

 

*Na uku 3*

*kullun yana kusantar lahira yana nisantar duniya amma duk da haka baya damuwa da lahira kamar yadda yadamu da duniya Bai san makomarsa ba shin aljannace ko wutace.*

 

*GASKIYA*

*Babu abunda xai amfaneka sai sallarka/ki*

 

*Duniya kwana 3 ce*

*Jiya: munganta baxata dawoba*

*Yau: muna cikinta baxata dauwama ba xata wuce

 

*Gobe: bamusan ina xamu kasanceba.*

*ka gaisa da mutane, kayimusu afuwa kayi sadaka domin ni da kai dasu duk Matafiyane bissalam.*

 

Allah Ya Bada Nasara Cikin Rayuwa.

Share

Back to top button