Shi Addini a Gurin ALLAH (S.W.T) Kamar Kudi Ne (A Gurin Gwamnati), Gwamnati Tana Da Kudinta. 

LISANUL FAIDHA (Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi (R.A) Yana Cewa;

 

“Shi Addini a Gurin ALLAH (S.W.T) Kamar Kudi Ne (A Gurin Gwamnati), Gwamnati Tana Da Kudinta,

 

Da Zarar Tana Son Ta Kawo Wani Sabon Tsari. (Takardan Kudi) Zata Yi Sanarwa (Notice) Cewa;

 

Kudi Mai Kala Kaza-Da-Kaza Zai Daina Aiki Daga Watan Kaza Da Ranar Kaza, Sabon Tsari (Na Kudin) Zai Fara Aiki Saboda Haka Duk Wanda Yake Da Tsohon Kudi Ya Je Ya Chanja Tun Kafin Mu Rufe Chanjin.

 

Wai Shin Idan Wani Mutum Ya Ce; Ni Kam Ban Ga Laifin Wannan(Tsohon) Kudin Nawa Ba Saboda Haka Ba Zan Chanza Ba, Idan Ya Je Sayen Wani Abu Za’a Kar6a Kuwa???

 

Amsa Ita Ce; Ah Ah! Jefarwa Za’a Yi.

 

To Haka Misalin Addini Yake a Gurin ALLAH(S.W.T).

 

Addinin Guda ‘Daya Ne a Gun SHI(ALLAH), Yana Turo Manzonninsa Da Shi, Wanda Duk Aka Turo Su Da Shi Zuwa Jama’arsa Zai Isar,

 

Da Zarar Ya Tafi, Sai ALLAH Ya Turo Wani Da Aika Ya Ce; Ya Ku Jama’a! ALLAHn Da Ya Turo Muku Wancan Manzo, Shi Ne Ya Turo Ni, Ku Zo Ku Bini Ku Samu Abin Da Baku Samu Ba Agun Magabacina.

 

A Haka Har ALLAH Ya Turo ANNABI MUHAMMADU(S.A.W) Wa Dukkan Duniya Baki ‘Dayanta, ANNABI ISAH(A.S) Shi Ne Na ‘Karshen Zuwa Kafin Zuwan MANZON ALLAH(S.A.W) Shima Yayi Ishara Da Zuwan SHI(S.A.W).

 

Da Wannan Muke ‘Kiran Dukkan Wanda Yake Ganin Kamar Yana Akan Addinin ANNABI MUSA(A.S) Ko ISA(A.S),

 

Cewan Addinin Da ANNABI MUHAMMADU (S.A.W) Ya Zo Da Shi Ya Bayyanar(Wato Islam) Shi Ne Fa Addini a Gun ALLAH, Yanzu Zamanin ANNABI MUHAMMADU(S.A.W) Ne Shi Ne Annabin Karshen Da Babu Wani Annabi Ko Manzo Da Zai Zo a Bayansa.

 

Saboda Haka Su Dawo Cikin Musulunci Tun Kafin Lokaci Ya ‘Kure, Mutum Ya Je Ya Ce; Zai Yi Chanji Ace Masa Ai An Rufe Chanji(Waton a Lahira Kenan), Shin Bai Ji Notice Na Zuwan Annabin ‘Karshen Zamani Bane???

 

Ai Duk Wanda Bai Bishi Ba To Ba Addinin ALLAH Yake Ba”.

 

MUN GODE SHEHU(R.A)

 

MU DAI FATANMU A KULLUM SHI NE

 

ALLAH YA ‘KARAWA MAULANMU SHEIKH(R.A) LAFIYA DA NISAN KWANA, YA BAMU ALBARKARSU, AMEEEEN

Share

Back to top button