Shugaba Tinubu Ya Taya Sheikh Dahiru Bauchi Murnar Cika Shekaru 100 A Duniya.

Shugaba Tinubu Ya Taya Sheikh Dahiru Bauchi Murnar Cika Shekaru 100 A Duniya

 

Shugaban ya bayyana Shehin Malamin a matsayin wata Fitila da ta bayar da gudunmuwa wajen haskaka koyarwar Addinin Musulunci da yaɗa kyawawan ɗabi’u a Najeriyar mu ta yau.

 

Shugaban ya kuma gode wa jagoran darikar Tijjaniyya bisa sadaukar da rayuwarsa wajen yada ilimi da bunkasa kyawawan dabi’u ga ‘yan Najeriya.

 

A wani mataki na nuna murna ga cikan malamin shekaru dari a duniya, shugaba Tinubu ya yi wa Shehin Fatan tsayin rai tare da gamawa da duniya lafiya.

 

Alhamdulillah, Masha’Allah

Share

Back to top button