SHUGABAN MASU BADA FATWA, TA NAJERIYA KUMA SHUGABAN MAJALISAR MALAMIN TA NAJERIYA (Mufti Of Nigeria).

SHUGABAN MASU BADA FATWA, TA NAJERIYA KUMA SHUGABAN MAJALISAR MALAMIN TA NAJERIYA. (Mufti Of Nigeria).

 

Maulana Sheikh Ibrahim Saleh Al-Hussainiy Maiduguri Yana Cewa:-

 

“Ka Sani Masana ALLAH(Sufaye) Su Suka Fi Mutane Riko Da Hukunce–Hukuncen Shari’ah, Kuma Duk Wanda Yake Da’awar Bin Sufaye Tare Da Watsar Da Shari’ah, Toshi Da’awar Kawai Yake Yi a Wannan Hanya, Kuma Baya Bakin Komai a Ciki”

 

Imam Junai’du (Shugaban Sufaye) Yana Cewa:“Dariku Dukkansu Abin Toshewa Ne Ga Masu Su Sai Wanda Ya Bi Sawun Manzon ALLAH (S.A.W)”.

 

Yan Qara Da Cewa:“Kuma Duk Wanda Bai Haddace Al-Qur’ani Ba Kuma Bai San Hadisi Ba, Ba’a Koyi Dashi a Hanyar Sufaye, Domin Ilimin Mu Wannan Abin Kayyadewa Ne: Da Kitabu Da Sunnah”,

 

HAKA NAN:-

 

Abu Hafs (R.A) Yana Cewa“Duk Wanda Baya Auna Ayyukansa Da Zantukansa a Kowane Lokaci Da Qur’ani Da Sunnah, Kuma Baya Tuhumar Tunanensa (KHADIRI) To Ba’a Kirga Shi a Cikin Littafan Mazaje (Sufaye)”,

 

WANNAN SHI NE HAQIQANIN SUFANCI!

 

YA ALLAH! KA QARA TABBATAR DA DUGA-DUGANMU AKAN WANNAN TAFARKIN NA SUFANCI, AMEEEN.

 

Share

Back to top button