Shugaban Masu Fatwa A Najeriya Maulana Sheikh Sharif Ibrahim Saleh Al Hussaini Tare Da Sheikh Dahiru Usman Bauchi RA.

BA ZASU TABA KUNYATA BA, SABODA BASU BIYO HANYAR YAUDARAR KAI BA.

 

Idan da sunajin kunya, idan da suna tsoron ALLAH, to Maluman bariki da suka yi amfani da Addini wajen tallata ‘yan Takara daga shekarar 2015 zuwa yanzu, bai ma kamata ace ko da iyalansu sun aminta dasu a addinance ba, balle kuma azo ga batun mabiya, saboda yadda suka zambaci mabiya da sura ta addini, karshe kowa ya fahinci maslahar kansu kawai suke karewa, domin babu guda cikinsu da ya taba nuna damuwarsa akan halin firgici, yunwa da ukuba da al’ummar Arewa suka tsinci kawunansu ciki.

 

Amma kamar yadda masu iya magana ke cewa “A DADE ANAYI SAI GASKIYA” wadannan jagorori namu tun bayan samun yancin kai suke gwagwarmayar Da’awa da bayar da Ilmi, sun rayu da Gobnatoci dadama na Mulkin soja da farar hula, amma babu guda da ya tankwarasu daga barin gaskiya zuwa son zuciyarsa, sai dai shedar da akayi musu shine “SUKAN FADAWA KOWACCE GOBNATI GASKIYA, KUMA KOFARSU TA BAYAR DA SHAWARA A BUDE TAKE KO DA YAUSHE GA DUK WANDA YA KUSANCESU”.

 

• Kowa yaji yadda Maulana Sheikh Tahir (R.T.A) yayi ta kira ga Gobnati akan halin da talakawa ke ciki.

 

• Kowa yasan yadda aka dauki Shekaru ana ta sauke Kur’ani a Zawiyyar Maulana Shariff duk domin neman dai-daituwar al’amura a kasarnan.

 

SABODA HAKA, SUN GIRMI SU TALLATA WANI DAN TAKARA, SUN KUMA GIRMI WANI YAYI ZATON CEWA ZUWAN WANI TANKARA GARESU KAMAR ALAMACE TA NUNA SUN AMINCE MASA, DOMIN SU KIWONSU BA IRIN NA MALAMAN BARIKI BANE, BAL DAI SU KOWA MA NASU NE. ALLAH YA KARA TSAWAITA MANA JINKIRINSU, MU CI GABA DA DIBAR MADADI GARESU.

 

Daga; Muhammadu Usman Gashua

Share

Back to top button