SIRRIN GANIN ANNABI SAW: Idan Kasa Son Ganin Manzon Allah SAW Ka Karanta Rubutun…

SIRRIN GANIN ANNABI SAW

 

Munyi alqawarin kawo fassarar faidhul Ahmadiy na haihuwar Annabi SAW, kuma mun kawo shi cikin sigar tambayar yan’uwa da bada tukuici ga wanda yayi nasarar bada amsa daidai, sannan munyi rubutu mai taken MAULIDIN ANNABI daga na daya zuwa na hudu. Toh abinda yayi saura shine MU’IJIZAR ANNABI da kuma SIRRIN GANIN SA ido da ido ko a mafarki, sirrin zan bayar yanzu da iznin shehu Abulfathi RTA.

 

Amma kafin in bada sirrin, ya kamata yan’uwa su san rabe-raben dake cikin ganin Annabi SAW. Owaisul Qarni yace sahabbai basu ga/san Annabi ba, abubakar ne kawai yayi kokarin ganin/sanin inuwar Annabi SAW. Magana yayi musu da harshen zati, kuma ishara ne garemu na baya akan muyi kokarin riskar ma’arifa (haqiqa) cikin lamarin Allah da Annabi SAW domin muyi gam da katar da qwayar shari’a ba bawo ba.

 

Zan bayar da sirrin bisa matakin musulunci guda uku, wato ISLAM (Musulmi), IMAN (Mumini) da kuma IHSAN (Arifi), duk wani masoyin Annabi yana cikin daya daga wannan muqamin.

 

1. Idan kai musulmi ne amma baka karbi dariqar tijjaniya ba, ga sirrin ganin Annabi SAW. Ranar lahadi zaka karanta ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WA SALLIM sau 92 bayan kowace sallar farilla, sannan in zaka kwanta kayi salatin sau 1,111, haka zaka yi har kwana 7, yayin kwanciyar ka, ka shagala da tunanin kyawawar halaye da siffofin Annabi da ka sani, a haka har bacci ya kwashe ka, da iznin Allah zaka ga Annabi a mafarki ko ido da ido kafin kwana bakwai din nan, gwargwadon abinda Allah ya nufe ka da samu daga falalar sa.

 

2. Idan kai batijjane ne amma baka yi tarbiya ba, ga sirrin ganin Annabi SAW. Zaka lazumci karanta salatul fatihi sau 535 bayan sallar asubah da sallar la’asar, in zaka kwanta kayi jauharatul kamali kafa 12, amma da alwalla kuma a wuri mai tsarki, kayi haka har tsawon kwana 7 ko 21 ko 41, zaka sadu da Annabi, zaka samu shirya zuwa ga sahihin shehin da zai maka tarbiya, zaka samu saduwa (wusuli) yayin tarbiyar cikin sauqi.

 

3. Idan kayi tarbiyatul azkar, toh aikin nan kwana 41 zaka yi, zaka fara ranar lahadi bayan kowacce sallar farilla kamar haka:

A. Sallar Asuba: ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN ALFATIHI LIMA UGLIQA sau 1000.

 

B. Sallar Azahar: ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN ALKATIMI LIMA SABAQA sau 1000.

 

C. Sallar La’asar: ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN NASIRIL HAQQI BIL HAQQI sau 1000.

 

D. Sallar Magriba: ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN ALHADI ILA SIRADIKAL MUSTAQEEM sau 1000.

 

E. Sallar Isha’i: ALLAHUMMA SALLI ALA SAYYIDINA MUHAMMADIN WA ALA ALIHI HAQQA QADRIHI WA MIQDARIHIL AZEEM sau 1000.

 

wanda duk yayi wannan zai samu FATHUL AKBAR wanda shine karshen kyautar da batijjane wanda yayi tarbiya zai samu daga Allah.

 

Ina tawassali da soyayyar da kuke yiwa Annabi SAW, in samu yarda da soyayyar shehu Abulfathi gami da hidimta masa hissan wa ma’anan, Alfarmar Maulana sayyidina Rasulillah SAW. Amiin

 

✍Sidi Sadauki

Share

Back to top button