SIRRIN MALLAKAR MIJI A DAKIN AURE: Yar Uwa Karanta Sirrikan Rike Mijin Aure.

SIRRIN RIQE MIJI

 

A cikin abubuwan da zan lissafo din nan, dole daya daga cikin su sai ya baki nasara wurin riqe mijin ki, musamman Number 1 da 7, ki kula dasu sosai.

 

1. Ki riqe ibada, ki fifita Allah akan komai, ya zama shine farkon wanda kike tunawa yayin damuwa ko farinciki.

 

2. Yawan yiwa miji godiya in ya kawo cefane ko in yayi miki kyauta tareda fatan alheri gareshi. Da Gaishe shi tamkar kina gaida uba (ki durkusa), da Yawan bada haquri koda kece kike da gaskiya.

 

3. Girmama yan’uwan sa da jan su a jiki wurin zolaya da fara’a da son nuna damuwa a kansu, da girmama abokanan sa kina kiran su UNCLE B, UNCLE GWARZO da sauran su, su da kansu zasu ce matar ka tana da biyayya da girmama na gaba. Zasu kare ki in yaso ya ɓata miki suna, zasu yaqi duk wacce zata zo tayi kishi dake.

 

4. Tattalin kayan abinci yayin girki (koda kinsan mijin ki mai arziki ne) sannan kar kiyi wasa da yin abinci a lokacin da yake buqata koda ke baki ji yunwa ba. Kuma ki yawaita dafa mai abinda yafi so koda ke abin baya birge ki, sai ki dafa abinda kike so inda hali.

 

6. Nuna damuwa idan kika ga yana cikin bacin rai ko in ya dawo fuskar sa a ɗaure, kar kiyi fushi kice dake yake, abubuwan da maza suke fuskanta a waje wallahi sunfi qarfin hankalin ki, babu kuma inda suke tsammanin samun farinciki sai wurin ki madam.

 

7. Fesa turare da yawan rufe jikin ki. Abin nufi, Kar ya saba ganin suffar ki koda yaushe, yin haka ne zaisa jikin ki ya dinga birge shi duk lokacin da ya ga halittar ki. Amma in ya saba ganin qirjin ki da sauran wurare anytime, toh kisani sha’awa kesa suffar mace ya birge namiji, idan baya yanayin sha’awa, jikin naki ma zai iya bashi haushi (musamman in jikin ya fara saki).

 

Ba birgewa bane yadda naga mata sun mayar da hankalin su wurin son barin tsiraicin su a waje ga mazajen su. Wallahi ko kece kika ga halittar sa ba a lokacin da kike sha’awar sa ba, sai kinji wani dum-dum a zuciyar ki.

 

Sabawa miji da ganin tsiraicin ki shi yake sa wasu mazan lura da suffar mata a waje (dan yaga wacce ta fiki ko kika fi). Amma Idan har ba ɗan iska bane, yadda kike always cikin kamala haka zai so ace sauran mata na waje suke, dan haka in yaga mace cikin tsiraici, Automatically zai ce MATATA TAFI WANNAN KAMUN KAI.

 

Matan aure, Please ku koyi rufe suffar ku cikin abaya ko hijabi ko sutura mai kamala.

 

Ki birge mijinki da murmushin ki, da kwalliyar fuskar ki, da iya hira, da sanin yaushe ya dace ki tambaye shi abu kaza da kaza (ba koda yaushe ake tambayar miji abu ba), ki saba masa da qamshin turaren ki, domin qamshi baya tsufa amma jiki yana tsufa, ki shagwaɓa shi da halin ki.

 

Lastly ki nisanci wayar sa ko any private life dinsa, shawara kyauta na baki domin QAZANTAR DA BAKA GANI BA, TSAFTA CE!

 

✍Sidi Sadauki.

Share

Back to top button