Soyayyar Annabi Ta Samarwa Wasu Daga Cikin Halittu Darajoji Da Muqamai A Wajen Allah Ba Tare Da Sunyi Sallar, Azumi Da Zakkah Ba.

A cikin Tarihin ANNABI S.A.W An samu halittu da dama wadanda suka samu darajoji da muqamai awajen Allah da ANNABI S.A.W ba tare da sun taba yin sallah ko azumi, ko kuma wani aikin ibada ba, Sai dai Domin sun nuna SOYAYYARSU GA ANNABI S.A.W

 

MISALI

DUTSEN UHUDU:- ANNABI S.A.W yana cewa “Uhud dutse ne Wanda YAKE SONMU muma kuma MUNA SON SHI”. Kunga kenan dutsen Uhudu ya samu babban rabo.

 

A KUTUTTUREN DABINO:- Wanda yayi kuka saboda tsananin Shauqi da Qaunar ANNABI S.A.W Kuma ANNABI S.A.W ya yarda dashi

 

Gashi anan duniya amma yana chan Annabi ya dasa shi agidan ALJANNAH.

 

BURAQAH:- Wacce ya hau adaren ISRA’I DA MI’IRAJI Ta kasance acikin ‘Yan uwanta Burakoki, amma ta rame bata ci bata sha saboda tsananin Bege da tunanin ANNABI S.A.W. Shiyasa Mala’ika Jibreel (AS) ya zabo ta ya taho da ita domin taga MASOYINTA ANNABI S.A.W. Kuma kafin ya hau bayanta sai da ta nemi wasu alfarmomi guda biyu awajensa ANNABI S.A.W. TACHE: “Ya Jibreelu ka gaya ma Wannan Masoyi, ma’abocin fuska mai kyau da Qyalkyali, INA SO YA SANYA NI ACIKIN CETONSA.. KUMA INA SO YA LAMUNCE MIN IN ZAMA ABIN HAWANSA AFILIN ALQIYAMAH”. Nan take ANNABI S.A.W yace “NA LAMUNCE MIKI”.

 

KOGON DA YA SHIGA: Aranar yakin Uhud Har yanzun nan Kogon yana Qamshin jikin ANNABI S.A.W.

 

QISSAR MUTUMIN NAN: mashayin giya wanda aka yi masa haddi har sau biyu. Da yazo akaro na ukun sai Sayyiduna Umar zai tsine masa. Sai ANNABI S.A.W yace “KYALE SHI YA UMAR. HAKIKA SHI YANA QAUNAR ALLAH DA MANZONSA”..(SAWW).

 

ALLAH SHI QARA MANA SON ANNABI S.A.W YA SAMU A CIKIN CETONSA (S.A.W). AMIIN

Share

Back to top button