SU WAYE ƳAN HAƘIƘA NA GASKIYA CIKIN DARIKAR TIJJANIYYA ??

SU WAYE ƳAN HAƘIƘA?

 

Gargadi: wannan rubutun bashi da alaƙa da wani bayan ni.

 

Babu wani abu da ke kawo saɓani da haifar da rabuwar kai cikin masu da’awar FAIRA da kuma ƴan FAIRA na gaskiya kamar kalmar HAƘIƘA. Yayin da wasu suka yi wa wannan kalmar mummunar fahimta saboda wasu dalilai da suka bayyana musu a zahiri, misali yadda ake sifffanta wasu mutane masu wani aiki da ya saɓawa shari’ah da ƴan hakika, da kuma yadda gama garin mutane suka fahimce ta kuma suke fassara ta.

 

Abu mafi al’ajabi shine, har cikin da’irar ƴan FAIRAR na gaskiya, wasu sun wayi gari suna kyamar wannan kalma, kuma basa so ko da wasa a alaƙanta su da ita balle a jingina musu.

 

Cikin wasiƙar da Shehu da yayi ta Risalatul Muntaqim, ya ambaci cewa akwai matasa da tuni sun manta ɗanɗano na sha’awa kuma har ta kai ga akwai wanda har manta matan su ma na Aure suke, saboda tsanin zauƙi da suka samu na Allah, basa zuwa wajen matan ma sai an musu izinin su tafi, wasu ma sai da tilastawa, saboda sun bar komai, da kowa, sun tare a wajen Allah. To wannan wata siffa ce ta ƳAN HAƘIƘA na gaskiya. Wannan kuwa ya saɓa da HAƘIƘAR da mutane ke da’awa yanzu wacce sha’awar ce ma ke musu jagoranci.

 

Saboda tsabar daɗin zauƙi na Allah da ƴan HAƘIƘA suka samu, to ni ban san masu kyautatawa halittu zato ba da kuma cikakkiyar himmar Wuridi da ƙarin nafiloli bayan na Farilla, da zama da kowa tsakani da Allah, wannan kuma ya samu asali ne saboda sirrin da suka riska na maida komai asalin sa, da kuma ganin komai a asalin sa har ma da fahimtar hikimar komai cikin nufin mai komai.

 

Idan wasu suka ɗauka cewa HAƘIKA iskanci ce, da raina Allah da Manzonsa, da kuma keta shari’ah, to lallai za’a iya musu uzuri bisa lura da yadda wasu masu da’awar wannan tafiya suke, wanda ba ɓoyayye bane.

 

Shi ɗan Haƙiƙa na asali idan aka ambaci Allah akwai wanda sai yayi mintoci bai ma san inda yake ba, saboda nauyin girman Allah da ke zuciyar sa, duk ɗan HAƘIƘA na gaskiya idan aka ambaci Manzan Allah fita yake cikin hayyacin sa, saboda an cire masa nustuwa da tunanin duk wani abu bayan Manzan Allah, wannan kuma shine haƙiƙanin nutsuwar zuciya.

 

Su ƴan HAƘIƘA na gaskiya sun gama narkewa cikin Allah, jin su, ganin su, tafiyar su, da kuma ɗamkar su duk da Allah su ke, kamar dai yadda Hadisi ingantacce ya tabbatar. Sun bawa Alllah dukkanin su, saboda haka sai Allah ya zama komai na su. Basu da komai sai Allah, basu san komai ba sai Allah, kuma basa sha’awar komai sai Allah.

 

Allah ya yarda mu zama ƳAN HAƘIƘA na gaskiya. Amiin Yaa ALLAH.

 

Ibrahim Sabo Al-Musaddady

Share

Back to top button