SUFANCI SHINE HANYAR TSIRA DON SAMUN HANYAR ZUWA GA ALLAH SWT.

KAI DA KAKE DA TABBAS, YAUSHE ZAKA BIYEWA KHUDBAR YAN YAUDARA..?

 

AUNA WADANNAN ABABE GUDA 2 A MIZANIN TUNANINKA.

 

1- Shekaru sama da 45, ana yakar Shehu Tijjani (R.T.A) da Darikarsa da duk wani abu mai muni da tunani zai iya hakaitowa na dangogin kage, sharri, kazafi , batanci da sauransu, amma dai abinda Darikar ta ginu akai tun jiya har zuwa yau shine “Istigfari, Salati, Hailala”, har kullum kuma su wadannan masu yakar kallon batattu suke mana, kuma makomarmu ta lahira itace wuta a irin hukuncinsu.

 

2- A tsawon wadannan Shekarun kuma su babban abinda suka shahara da shi wanda aka kiyaye wajen babban jagoransu shine “Siyasa Tafi Sallah” gashi dai idan lokacin kamfen yayi, Malamansu na shiga wannan harka a dama da su, su yi ta bayar da fatawowi, tare da tallata yan takarkaru ta sigogi mabambanta.

 

ABIN LURA SHI NE.

 

• A Unguwar da kake, garinku ko kuma yankinku, mai yiwuwa ka gani, kuma kaji labarin yadda idan Tijjanawan da suka kyautata riko da ita, suka zo komawa zuwa ga ALLAH kalmarsu ta karshe ke zama “KALMAR SHAHADA” sannan wata alama da ke nuni akan ALLAH ya yarda da su shine “Duk yadda jikkunansu ya dauki tsawon lokaci a cikin kasa, idan wani aiki ya biyo ta kan kaburburansu akan sami jikkunansu lafiya kalau”.

 

• Amma su kuma da mun lura, shin abinda suka dauka gaba da Sallah (SIYASA) suke bautar da kawunansu ga ‘Yan Siyasa a kai ta hanyar bambadanci, tumasanci, shin Masallata na ganin wata Masalaha ga Duniyarsu cikin Siyasar, shin tsakanin Musulmi da wadanda ba Musulmi ba su waye suka fi cutuwa cikinta, shin su wa ake kashewa a kullum dalilinta, shin siyasar ta haifarwa Musulmi wata Maslaha a duniyarsa ta yau kafin aje zuwa ga lahirar?

 

SHIN YA DACE WADANDA AKAN HARKAR DUNIYARSU MA TAWAYA TA BAYYANA TATTARE DA SU, SU YAUDARE KU GA BARIN HANYAR NEMAN LAHIRARKU ALHALI AN GANI MILYOYI SUN SAMU DACEWA AKAI DA YAQINI..?

 

ALLAH YA SA MU DACE…!

 

Daga: Muhammadu Usman Gashua

Share

Back to top button