Suffofin Yan Darika A Cikin Hadisin Manzon Allah SAW.

SUFFOFIN YAN DARIKA A CIKIN HADISIN

ANNABI (SAW).

 

Daga Umar Chobbe

 

Annabi (S.A.W) yace wallahi Allah zai tashi wadansu jama’a ranar Alkiyama, haske yana tashi a fuskokinsu, suna zaune akan mumbari lu’u-lu’u, mutane suna buri ina ma sune wadannan jama’a alhalin su wadan nan jama’ar ba Annabawa bane, ba kuma shuhada’u bane’

 

Sai mai ruwaya yace, sai wani balarabe kauye yace:-

“Ya ANNABI siffanta mana su, ko masan kamanninsu Mana,

 

Sai ANNABI (S.A.W) yace ai sune mutanen da suke soyayya dan Allah daga kabila daban-daban kuma garlnsu daban-daban, kuma suna taruwa ne akan zikiri Allah, suna kuma ambatan sa.

 

Wannan Hadisi Dabarani ne ya ruwaito shi da isnadi mai inganci a wajen Abu darda’i (R.T.A) karanta Hadisin..

 

ﻭﻗﺎﻝ ﺭﺳﻮﺍﻟﻠﻪ ﺻﻠﺊ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ : ﻟﻴﻌﺜﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﺃﻗﻮﺍﻣﺎ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎ ﻣﺔﻭﺟﻮ ﻫﻬﻢ ﺍﻟﻨﻮﺭﻋﻠﺊ ﻣﻨﺎﺑﺮﺍﻟﻠﻮﻟﻮﻳﻐﺒﻂﻫﻢ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻟﻴﺴﻮﺍﺑﺄﻧﺒﻴﺎﺀﻭﻻ ﺷﻬﺪﺍﺀﻗﺎﻝ : ﻓﺠﺚ ﺃﻋﺮﺍﺑﻲ ﻋﻠﺊ ﺭﻛﺒﺘﻴﻪ، ﻓﻘﺎﻝ ﻳﺎﺭﺳﻮﻝ ﺍﻟﻠﻪ : ﺣﻠﻬﻢ ﻟﻨﺎ ﻧﻌﺮ ﻓﻬﻢ ﻗﺎﻝ : ﻫﻢ

ﺍﻟﻤﺘﺤﺎ ﺑﻮﻥ ﻓﺊ ﺍﻟﻠﻪ ﻫﻦ ﻗﺒﺎﺀﻝ ﺷﺘﺊ ﻭﺑﻼﺩ . ﺷﺘﺊ

ﻳﺠﺘﻤﻌﻮﻥ ﻋﻠﺊ ﺫﻛﺮﺍﻟﻠﻪ ﻳﺬﻛﺮﻭﻧﻪ . ﺭﻭﻩ ﺍﻟﻄﺒﺮﺍ ﻧﻲ ﺑﺎﺳﻨﺎﺩ ﺣﺴﻦ .

 

Yan Darika mu godewa Allah da muka sami kammu cikin darikan Tijjaniyya Alhamdilillah.

 

Allah Ya kashemu Cikin ta Bijahi S.A.W

 

Wanda kuma yake Zagin Mu Allah ya Ganar dashi ya Fahimci Gaskiya don ya dandana Madarar da muke tsosawan Bijahi S.A.W. Amiin

Share

Back to top button