TA’ALIKI AKAN MAGAGGANUN MANYAN MALAMAI TARE DA SAYYADI UMAR CHOBBE (Kashi Na Takwas 8).

TA’ALIKI AKAN MAGAGGANUN MANYAN MALAMAI TARE DA SAYYADI UMAR CHOBBE (Kashi Na Takwas 8).

 

PROFESSOR IBRAHIM AHMAD MAQARI YANA CEWA:-

 

MUTANE BASU FAHIMCI MA’ANAR KARAMA BA, YACE ITA FA KARAMA BAWAI MAI KARAMAR NE YAKE YIN TA BA

 

A’A MA’ANARTA ALLAH YAYI KARAMCI GA WANI BAWANSA

 

PROFESSOR YACI GABA DA CEWA SHIYASA DUK WANDA ZAI YI KARAMA BAI MA SAN YAYI BA, SABANIN MU’UJIZA. WACCE ITA DUK WANDA ZAI YI TA SAI YASAN YAYI

 

PROFESSOR YACI GABA DA CEWA AKWAI WATA HIKAYA DUK DA BAN SAN CIKAKKEN ASALIN TABA

 

ANCE WATA RANA “SIDI ABDUL QADIRI JAILANI” (R.T.A) SUN DAN SAMU SABANI DA IYALANSA AGIDA WATO (MATANSA)

 

SAI YA FITA YATAFI CIKIN DAJI YA SHIGA HALWA DA YA JE INDA ZAI YI HALWAR SAI YA TADDA WASU MUTANE SUMA SUNYI YAN BUKKOKINSU ACIKIN DAJIN. SAI SHIMA “SIDI ABDUL QADIR” YAYI TASHI BUKAR AGEFEN TASU

 

TO DUKKANSU SUNA AZUMI SABODA DAMA KA’IDAR HALWA KENAN MASU YINTA SUNA KASANCEWA DA AZUMI SAI LOKACIN BUDA BAKI YAYI DUK SAI SUKA HADU.

 

SAI DAYA DAGA CIKINSU YAYI ADDU’A SAI GA ABINCI SUKA CI SUKAYI BUDA. BAKI DASHI

.

RANA TA (2)SAI DAYAN DAGA CIKIN SU SHIMA YAYI ADDU’A SAI GA ABINCI SUKA CI

 

ARANA TA ( 3) GA LOKACIN BUDA BAKI YAYI SAI SUKACE SIDI ABDUL QADIR SHINE ZAI YI MUSU ADDU’A SU SAMU ABIN BUDA BAKI

.

SAI SIDI YAYI ADDU’A, SAI GA ABINCI SAI MUTANEN NAN SUKACE SU BAZASU CI WANNAN ABINCI BA SAI YAGAYA MUSU ISMILLAHINDA YA KARANTA WANNAN ABINCIN YAZO. SAI SHEHU YACE A’A KU DA KUKAYI NAKU NA TAMBAYEKU NE?

 

SUKACE AI SU ALAMBARA BAZA SU CI BA SAI YAGAYA MUSU IRIN ADDU’AR DA YAYI

 

SAI SIDI YACE TO SHIKENAN ZAN GAYA MUKU AMMA DA SHARADIN NIMA SAI KUN GAYAMIN ABINDA KUKA KARANTA SANNAN SÀI SUKACE EH ZASU GAYA MASA

 

TO SHIKENAN SAI YACE MASU SHI ABINDA YAYI SHINE ROKON ALLAH YAYI YACE

 

YA ALLAH UBANGIJI KADA KA TOZAR TANI INA ROKONKA DA ABINDA WANNAN BAYIN NAKA SUKA ROKE KA DASHI KABIYA MIN BUKATATA, SAI KAWAI GA ABINCIN YAZO

 

BAYAN YA BASU LABARIN YACE TO KU ME KUKAYI NE ?

 

SAI SUKACE MU MUN ROKI ALLAH NE MUNYI TA WASSULI DA WANI WALIYYIN ALLAH WANDA ANSANAR DAMU SHI CEWA DUK WANNAN ZAMANIN BABU WANI WALIYYIN DA YAKAISHI ADORAN KASA.

 

SHINE MUKA ROKI ALLAH ALBARKARSHI ALLAH YA CIYAR DAMU

 

DA SIDI YAJI HAKA SAI YACE TO AI DA SAURANKU KUNFADI MIN AMMA BAKU FADI MIN SUNANSHI BA? SAI SUKACE SUNAN SHI ABDUL QADIRI JAILANI (R.T.A)

 

PROFESSOR YACE KUNGA ANAN SHEHU YAYI KARAMA AMMA BAI MA SAN YAYI BA

 

WATO ASHE DUK WANNAN ABUN DA AKAYI DUK ALBARKARSHI ALLAH YA CIYAR DASU SUNYI KAMUN KAFA DASHI AWAJEN ALLAH, KUMA ALLAH YACIYAR DASU HAR KWANA 3 SHI BAIMA SANI BA CEWA DUK DANSHI AKE CIYAR DASU

 

HAKA SUMA BASU SAN SHINE SUKE TARE DASHI BA AKE CIYARDASU DAN SHI BA.

 

PROFESSOR MUNGODE ALLAH YAKARA MAKA LAFIYA. DA NISAN KWANA DA KARIYA DAGA DUK KAN SHARRIN MASU SHARRI. AMEEEEEEEEN.

Share

Back to top button