Takaitacce Tarihin Khalifa Sheikh Tijjani Inyass RA

Takaitaccen Tarihin Khalifa Sheikh Ahmad Tijjani Inyass❤️

 

Babban Jaridar kasar Senegal mai suna Dakar News ta ruwaito cewa Khalifa Ahmad Tijjani Niasse daya ne daga cikin mutane masu alfarma da daraja a kasar Senegal, kuma babban masanin addinnin musulunci ne mai ra’ayin samar da masalaha ga zamantakewar al’umma, musulmai da wadanda ba musulmai ba.

 

Khalifa daya ne daga cikin ‘ya’yan Shehu Ibrahim Inyass RTA mai faidar tijjaniyya wanda ya asassa babban birnin madinatu Baye a Kaulaha dake kasar Senegal, sunan mahaifiyarsa sayyada Maryam. An haifi Khalifa Tijjani Inyass a shekarar 1932 miladiya a kauyen ‘Kusa’ dake nisan kilomita 9 daga Kaulaha.

 

Yayi karatun Alqur’ani a wajen malamansa na kasar Muritaniya da Senegal, ya haddace Qur’ani a hannun Sheikh Umar Turi, bayan nan ya dawo shingen mahaifinsa ya ci gaba da karatu inda ya koyi luggan larabci da ilimomin addini a hannun malamansa guda biyu, Sheikh Amadu Tiam da Sheikh Aliyu Cisse. Khalifa ya kasance dalibi mai matukar kokari da sa ido a karatu, bayan nan Khalifa ya tafi kasar misra inda ya karanta fannin adabin larabci da ilimomin addinin musulunci, har ya samu shahada a jami’ar Azhar.

 

Bayan ya dawo daga Misra ya zamo na hannun daman Shehu Ibrahim Inyass, duk tafiye tafiyen da Shehu yake yi zuwa kasashen waje dan yada addinin musulunci tare yake zuwa da Khalifa, saboda kwarewarsa a harsunan larabci da turanci da faransanci wajen furuci da rubutu.

 

Shehu Ibrahim Inyass yayi masa wasici da ya raya alqaryar da ake kira ‘Daru Mabiteen’ Shehu ya cika wannan wasici inda ya mayar da alqaryar sabuwa, kuma ya samar da hadin kai da fahimtar juna a wurin.

 

A tsawon rayuwarsa ya kasance mai himma wajen gina al’umma, yana yawan taimakon talakawa da mabukata. Yayi aiki tukuru wajen samar da cigaba a garin madinatu Baye, inda ya kirkiri ayyuka (Project) dan sabunta garin Madinatu Baye, a karkashin halifancinsa yayi gyara da fadada masallacin Madinatu Baye, ya gina katafaren masaukin baki wanda ake sauke daruruwar baki a ciki, shi ya farfado da kungiyar Ansarul Deen wanda Shehu ya kafa a shekarar 1940, ya gina gidaje na karatun Alqur’ani, ya gina makarantu da asibitoci masu yawa a nahiyoyi daban daban na kasar Senegal.

 

Bayan rasuwar Shehu Khalifa Tijjani Inyass ya himmatu wajen hidimtawa halifofin Shehu musamman Sheikh Aliyu Cisse da Khalifa Sheikh Abdullahi Inyass da Sheikh Hadi Inyass da Sheikh Ahmad dam Inyass.

 

Khalifa ya shahara wajen talifin littafai, ya rubuta littafai da dama kamar su ‘Zajrul Ikhwan’ wanda aka buga shi a shekarar 1978, ya kuma rubuta littafi akan alaqar Shehu Ibrahim Inyass da Najeriya mai suna ‘alaqatu Shehu Ibrahim Inyass bi Nigeria’ wannan littafin wani Farfesa a fannin lissafi mai suna Sambo Gan Luh a jami’ar Gaston dake Sant Luis a kasar Faransa ya fassara shi zuwa yaren farasanci a shekarar 2010.

 

Khalifa ya koma ga mahallicinsa yana da shekaru 88 a ranar 02 ga watan Augusta a shekarar 2020 a asibitin City WW a birnin Dakar, Senegal.

 

Muna rokon Allah ya lullube sa da rahamarsa, ya zaunar da shi a aljannarsa mai yalwa tare da Annabawa da sidsiqai da shahidai da salihan bayi amin.

 

Muna fatan Allah ya karawa kaninsa Khalifa Mahi Inyass wanda ya zamo halifa yanzu juriyar rashi da lafiya da tsawon kwana, ya saukake mishi wannan nauyin da ya daura mishi ya kuma katartar da shi akan wannan aiki amin.

 

Fassara : Rayyahi Sani Khalifa

Share

Back to top button