Takaitacce Tarihin Shahararen Malami Sheikh Tijjani Zangon Bare Bari Kano

Takaitacce Tarihin Sheikh Tijjani Usman Zangon Bare Bari Kano Kashi Na Daya (1).

 

MAHAIFIYARSA

 

Mahaifiyarsa kuwa sunanta hajiya rabi’atu ita kuma Macece kyakyawa kamar balarabiya farace sosai kuma mai madaidaicin tsawo, domin har tsufanta kai da kaganta kasan kyakykyawace mace ce mai kula da addini mai kunya, mai qarancin sutura, kuma bazaka ganta tatsaya atiti tana surutu da waniba har kuma tsufanta domin kuwa koma kayi mata magana atiti, sai dai kugaisa kawai tawuce, mahaifin hajiya rabi sananne ne kuma yasaba da mutane da dama, mutum ne mai’arziqi kuma mai riqo da addini, sunansa Abubakar maishago, mutum ne shima fari, kyakyawa, mai doguwar fuska da hanci har baka, gashi kuma dogo ne sosai. Kai daka ganshi kasan yahada nasaba da larabawa.

 

A lokacin shehu mujaddadi usman danfodiyo yana da wani aboki balaraben tumbuktu ta cikin qasar mali lokaci zuwa lokaci yakan ziyarci abokinsa sheshu usman a nan nageriya, to cikin irin wannan ziyara ne wani lokaci da yazo, a sannan kuma anan kano annada Ibrahim Alu sarauta kowa kuwa yasan alu yana da dan gantaka da sakkwato tawajen mahaifiyarsa, to bayan wancen balarabe shehun malami yakamala ziyararsa a sakkato, sai shehu Usmanu ya nemi ko zaizo kano yayiwa sarki da garin kano din addu’a.

 

Wannan malami ya amince yataho, daya iso kano sarki yaji daga inda yake, yaga kuma qimarsa na kasancewarsa babban malami sai ya karbe shi hannu biyu, Ya girmamashi, yakuma yimasa sauka ta manyan baki, kai harma ya aikawa sarakunan gumal da hadeja da kazaure kan suzo ayi musu addu’a.

 

Bayan sun zone sarkin gumel yaroqi sarki arziqi a kan shima yanaso malam yaje garinsa yayiwa garin addu’a, sarki ya amince, to bayan shehin malamin yaje ne, cikin irin hidimar da sarkin na wannan zamani yayi masa har da wata ƙwar-ƙwarar sarki wadda take bafulatana ce kyakyawar gaske, wadda sarki yaga ta dace da wannan balarabe, duk ya hada yabashi, wannan mata da wannan baqon balarabe sune suka haifi Abdullahi maishago (kakan mahaifiyar shehi malam Tijjani) shi dai wannan baqon balarabe kuma shehin malami sunan sa sidi Amal.

 

Shi dai malam Abubakar maishago ya dade a duniya, domin ya rayu sama da shekaru casa’in da wanin abu, kuma kamar yadda mukafada abaya mashahurine kuma mai kyawunhali, wannan ya tsallaka har ga kan mai dakinsa, wadda ta haifi shehi malam Tijjani, kuma ake kira iya dije, wadda it ace ta haifi hajiya rabi wadda ta haifi shehi malam Tijjani, kuma ita kadai ce diyar ta

 

Iya dije Allah S.W.T yayi mata arziqi da sutura kwarai da gaske, mai son malamai da taimakawa makaranta tare da qoqari wajen hidimtawa malamai kuma tana da wata al’ada wadda take itace duk juma’a takanyi abinci mai kyau na alfarma, ta hada da goro da turare da yan sauran kayayaki haka ta dinga kai wa gidajen manyan malamai na kano na wannan lokaci alal misali idan wannan juma’ar takai gidan malam umaru na madabo wata juma’ar kuma sai ta kai gidan malam Adhama, wata juma’ar kuma kamar gidan malam na jarqasa mai ashafa haka dai taketayi kusan duk malaman garin nan a wannan lokacin babu wanda bai san iya Dije mai alheri ce ba kuma da ita da mijinta malam Abubakar maishago yarsu kenan guda daya wato hajiya rabi ita kuma a sannan danta kenan daya shehi malam Tijjani.

 

To kamar dai yadda muka ambata abaya, bayan mahaifin shehi ya dawo daga waccan tafiya da yayi a sannan shehi nada kimanin shekaru biyar bayan ya dan zauna kadan saiya sauwaqewa iyalinsa wannan kuma wata hikimace ta ubangiji yadda zakaga sau dayawa zakaga wani abin ya afku sannan wani kan afku bayan wannan rabuwane da hajiya rabi tagama idda saita auri wani malami da akekira malam Ahmadu Tijjani mai kanwa wanda akafi sani da (Ahmadu madu) kuma shine (walidin) mahaifinsu malam lawan na shehi da Alhaji sani mumini da sauran ya’yansu mata.

 

Amma a wani kaulin ance Malam Usman sannan da wannan shauqi na kaunar Manzon Allah ya debeshi yayi niyyar tafiya hajji ya baiwa ita hajiya rabi zabi akan kodai ya sauwake mata ko kuma ta shirya sutafi tare da dansu to kamar yadda muka ambata a baya Allah bai nufa ba sai mahaifinta Abubakar maishago ya hanata saboda haka mijin ya sauwaqe mata kaga wannan sai ya zama alhairi ga kano da mutanan cikinta bama ya irin wadanda suke kewayen bakin kasuwa wadanda sukafi jiqewa sharkaf da ruwan albarka daya bubbugo daga wannan babban shehi Allah ya qara masa rahama amin.

 

Wannan kadan kenan daga cikin nasabar shehi da kuma taqaitaccen tarihin mahaifansa Allah yayi gafara garesu damu baki daya Amin.

 

Daga: Aliyu Rabiu Aliyu

Share

Back to top button