Takaitacce Tarihin Sheikh Aliyu Harazumi Hausawa Kano Kashi Na Biyu (2).

MAI TAMBARIN ZIKIRI DATTIJO MAI ABUN MAMAKI MAULANA SHEIKH ALIYU HARAZIMI HAUSAWA (RADIYALLAHU ANHU) (II)

 

A cigaba da kawo tarihin ƙasaitaciyar rayuwar Maulana Sheikh Aliyu Harazimi Hausawa (Radiyallahu anhu) Na tsaya inda nake faɗin Maulana ya fara ɗaukar karatu a wajen shahararren Malamin nan Malam Salihu a wajensa Maulana ya samu Alkur’ani mai girma.

 

A shekarar 1933 mahaifinsa ya ɗauke shi tare da babban yayansa Sheikh Muhammadu Mustapha da kuma ƙaninsa Sheikh Muhammadu Ghali mahaifin shahararren ɗan siyasar nan Aminu Ghali Hausawa. zuwa ga wani babban Sharifi da ke zaune a cikin birnin Kano, ana ce masa Baba Adakawa, domin a ƙaddamar da su. A cikin ɗarikar Tijjaniyya.

 

Bayan shekara uku da kai su wajen Sharif Baba Adakawa, mahaifin Maulana ya lura da baiwar Maulana da Allah ya keɓancce shi da ita wajen gudun duniya. Ya yi masa muƙaddamanci na ɗariƙar Tijjaniyya, 1936. A lokacin Maulana yana da shekara 17 ya fara zama muƙaddami…

 

Shehu ya fara halartar Jami’ar yaye manyan Mazajen duniya da lahira wacce take ƙarƙashin jagorancin Maulana Sheikh Abubakar Atiku Sanka (Radiyallahu anhu) A shekarar 1937 a lokacin Maulana yana da shekara 18..

 

A farkon shekarar 1940, Maulana Sheikh Usman Mai Hula (Ƙalansawi) ya bukaci Maulana Shehu Aliyu Harazimi (Radiyallahu anhu) Ya din ga zuwa ɗaukar karatu a makarantarsa ​​da ke unguwar Ɗiso. Maulana ya koyi Ilimin fikihun Malikiyya da usulul fiƙh da tafsirin Alkur’ani mai girma da nahawun larabci da adabi da kuma Sufanci.

 

Kamar yadda Maulana ya ba mu tarihin da kansa yace ya ɗauki karatu a wajen babban abokinsa Shehu Isa Mandawari, (Radiyallahu anhu) Ya karanta littattafan Hadisi da Larabci, da adabi, da fikihu, da Sufanci da tafsirin Alƙur’ani tare da shi. Sannan a cikin Malam Shehu akwai wani ɓoyayyan Malami wanda ake kira da suna Malam Ado, wanda yake a unguwar Kurna wanda tana cikin tsohon birnin Kano, Sannan yayi karatu a wajen Malam Muhammadu Inuwa.

 

Wacce shekarar ne aka kafa zawiya?, To dai Zawiya Mahaifin Maulana Shehu ne ya ƙafata a lokacin yana da dalibai masu yawa kuma yana koyar da su, a lokacin jama’a-jama’a suna zuwa ƙarɓar ɗarikar Tijjaniyya daga gurare daban-daban.

 

A shekarar 1915 aka kafa ta kafin zuwan Maulana wannan duniyar da shekara 4 a gidansu da ke unguwar Hausawa, cikin tsohon birnin Kano a tarayya Najeriya.

 

Allah ya bamu albarkacin sa. Amiin

 

Daga: Mujaheed M. Muh’d

Share

Back to top button