Takaitacce Tarihin Sheikh Aliyu Harazumi Hausawa Kano Kashi Na Daya (1).

MAI TAMBARIN ZIKIRI DATTIJO MAI ABUN MAMAKI MAULANA SHEIKH ALIYU HARAZIMI HAUSAWA (RADIYALLAHU ANHU)…(I)

 

“TAƘAITACEN TARIHIN MAULANA ABUL ANUWARU.”

 

“Asalin sunansa Aliyu Harazumi ya gaji sunan babban almajirin Sheikh Ahmed Tijjani (Abul Abbas,) (Radiyallahu anhu) An haifi Maulana Sheikh Aliyu Harazimi a ranar Alhamis 9 ga watan Zul Hijja a shekara ta 1336 a kalandar Musulunci a shekarar 1919 Miladiyya a unguwar Hausawa, cikin tsohon birnin Kano.

An haife shi a cikin iyali na ilmantarwa da jagoranci na addini. Mahaifinsa sanannen Malamin addini ne kuma muƙaddami na ɗariƙar Tijjaniyya, sunansa Shehu Muhammadu Sani, ɗan Muhammadu Dahiru ɗan Sarkin Shanu (lakabin sarauta na gargajiya, wanda aka ba shi alhakin karbar harajin shanu daga hannun Fulani makiyaya Hassan dan Sarki Ibrahim Dabo Sarkin Fulani na biyu a Kano daga ƙabilar Fulani Suluɓawa.”

 

“Mahaifiyarsa mace ce mai tsananin tsoron Allah, ana ce da ita Sayyada Maimuna, ƴar Malam Abdullahi Mai Panisau, ɗan Madakin na Kano Umar Na-Yaya, ɗan Alim Jibir, dan Liman Yati, dan Ahmadu Jandaro, wanda ya yi hijira. daga Mayo Belwa, garin Fulani wanda halin yanzu tana jihar Adamawa (Arewa maso gabashin Najeriya).”

 

“Na samu wannan tarihin daga wajen wani dattijo mai tarin shekaru. Na tambaye shi game da Maulana batun tasowarsa tun yana matashi abin da ya ce mun shi ne: Malam Aliyu Harazimi, mun samu bayyanin tun yana matashi. An ce ba’a taɓa jin ya yi zagi ba, ko ya yi faɗa irin na matasa ko ya fusata wani mutum. yace kullum cikin zikiri yake da tafiya neman Ilimin Addini.”

 

“Har ila yau, an ruwaito cewa a lokacin yana karami, duk lokacin da mahaifiyarsa za ta aika shi gidan dan uwansa, wanda yake a matsayin Madakin Kano, yana ɗaya daga cikin manyan ƴan majalisar masarautar Kano, An ce ya kan fashe da kuka don nuna rashin son haɗuwa da mutane masu fada a ji. Rashin son kayan alatu da rayuwar duniya ya taso da ita tun lokacin da yake matashi da kaucewa cudanya da hamshakan attajirai da manyan masu sarautar gargajiya duk da a cikin Iyalin ta ya fito.”

 

“A bisa al’adar gidan malamai, Shehu Aliyu Harazimi (Radiyallahu anhu) ya fara karatunsa na farko a gida a ƙarƙashin kulawar mahaifinsa, yana koyon karatun Alkur’ani, mai girma da Ilimin Fiƙihun makarantar Malikiyya da kuma Ilimin Sufanci na asali. Sannan ya ci gaba da karatun Alkur’ani a ƙarƙashin wani shahararren Malami da ake kira Malam Salihu.”

 

Allah ya bamu albarkacin sa. Amiin

 

Daga: Mujaheed M Muh’d

Share

Back to top button