Takaitacce Tarihin Sheikh Aliyu Harazumi Hausawa Kano Kashi Na Uku (3).

MAI TAMBARIN ZIKIRI DATTIJO MAI ABUN MAMAKI MAULANA SHEIKH ALIYU HARAZIMI HAUSAWA (RADIYALLAHU ANHU)..(III)

 

“A cigaba da kawo tarihin ƙasaitaciyar rayuwar Maulana Sheikh Aliyu Harazimi Hausawa, (Radiyallahu anhu) Na tsaya a inda na kawo jerin Malam Maulana.”

 

“Ziyarar Shehul Islam Maulana Alhaji Ibrahim Niasee (Radiyallahu anhu) A shekarar 1945 bayan komawarsa Kaulaha. Sheikh Abubakar Atiku, (Radiyallahu anhu) tare da Shehu Mai hula, tare da manyan Malaman Kano sun kai masa ziyara har garin Kaulaha. sun samu tarbiyyar ruhi daga Maulana Imamu Aliyu Cisse (Radiyallahu anhu)”

 

“Bayan dawowarsu Sheikh Abubakar Atiku (Radiyallahu anhu) Sun dawo da izinin tarbiyyar ruhi Maulana Sheikh Aliyu Harazimi

(Radiyallahu anhu) ya samu horon ruhi wanda aka fi sani da tarbiya a cikin shekarar 1946 a lokacin Shehu yana da shekaru 26 a ƙarƙashin jagoransa Sheikh Abubakar Atiku (Radiyallahu anhu).”

 

“A cikin shekarar 1947 ne Shehu Abubakar Atiku Sanka (Radiyallahu anhu) ya yi masa izinin gamamme na muƙaddamnci ɗariƙar Tijjaniyya dama a baya na faɗa muku cewa mahaifinsa yayi masa muƙaddamnci.”

 

“Sheikh Abubakar Atiku ya yiwa Maulana izinin komawa garin Nguru na jahar Yobe a arewacin Najeriya wajen Maulana Sheikh Muhammadu Gibrima, (Radiyallahu anhu) domin ya ci gaba da horar da ruhinsa, zaman sa a garin Nguru sai da ya kasance babban almajirinsa saboda baiwarsa duda ya tarar da almajirai a zawiyar.”

 

“Shehu Gibrima ya shahara da zamowa likitan zuciya. Ya zauna a gidan Sheikh Muhammadu Gibrima (Radiyallahu anhu) tare da sauran ƴan’uwan almajirai. Maulana ya zamo kullum cikin auradai sai dai ya kai matsayin da a ke kira al-Fat’ul-akbar (‘Mafi girman wulayyar haske’). Har ila yau, kuma ya wuce wasu muƙamai goma sha ɗaya na ruhi da aka sani da Sirr al-sirr (‘sirrin ciki’, a wata kuma ma’anar, ta nufin wani ƙololuwar muƙami wanda yake dandake ‘ruhi”; sanan muƙami yana kawai da ganin shugaba Sallallahu alaihi Wa sallama a farke.”

 

“Daya daga cikin mahimmanci ƙarin cigaba da Maulana Shehu Aliyu Harazimi (Radiyallahu anhu) Ya ƙara shiga, wanda ya zama ginshikin aikinsa, wanda ya yi a ƙarƙashin jagorancin Shehu Gibrima. Wanda ya dinga karanta Salatul Fatiha har sai da ya kai matsayin Fathul-akbar (‘Mafi girman haske’).”

 

“Kamar yanda muka samu daga bakin magabata makusantan Shehu mun naƙalto daga wajen su sun yi bayani game da jajircewar Maulana wajen neman Allah. An ruwaito cewa ya taɓa shiga Khalwa a ƙarƙashin jagorancin Shehin sa. An bayana cewa ya yi kwanaki masu yawa yana karanta auradan Yana cikin karanta su sai ya ga wata ƙura ta cika ɗakin daya yake ciki mai tsanani zafi, amman bai tsaya ba ya ci gaba da karanta auradainsa kamar yadda Shehunsa Sheikh Muhammadu Gibrima ya ce kada ya duba menene yake faruwa kuma kar ya koma da baya ko kuma ya fito ko duk abin da zai gani.”

 

“Sannan ance ya ga wani katon maciji a cikin dakin, wanda ya bayyana a cikin dare, amma bai cutar da shi ba, domin kawai yana son jin ƙamshin sunayen Allah.”

 

“Sakamakon wannan khalwa shi ne tun a daga wancan lokacin bai taba sha’awar wani abu da ya shafi rayuwar duniya ba , domin kullum cikin jin ɗanɗano zaƙin Ubangiji yake.”

Allah ya bamu albarkacin sa. Amiin YAA Allah.

 

Daga: Mujaheed M Muh’d

Share

Back to top button