TAKAITACCEN TARIHIN MAULANMU SHEIKH MODIBBO ALIYU JOBBO GOMBE

{TAƘAITACHCHEN TARIHIN MAULANMU SHEIKH MODIBBO ALIYU JOBBO GOMBE}

 

Sunan Sa Modibbo Aliyu, Amma Anfi Sanin Sa Da {Modibbo Joɓɓo} Dan Modibbo Abbdullahi (Shetiman Dukku) Dan Modibbo Ardo Haruna Jikan Modibbo Ardo Sambo Bodejo, Wato Sarkin Fulani Na farko A kasar Dukku, Sunzo Ƙasar Dukku Tun Kafin Jihadin Shehu Usman Dan-Fodiyo A Shekara Ta 1804.

 

Kamar Yanda Yazo A Tarihi, Sunzo Ne Daga Yammacin Kasar Sudan Wato Yankin {Kurdufan} Sun Biyo Yankin {Kanem Borno} Har Suka Tsaya A {Qatar Kalam} Wato Dukku A Yanzu, Inda Wasunsu Kuma Suka Wuche Garin Jama’are Dakuma Garin Shira, Wanda Duk Waɗannan Garuruwan Suke A Jahar Bauchi, Sannan Akwai Wadanda Suka Wuche Chan Garin {Jahun} Dake Jahar Jigawa.

 

{MAHAIFAR SA}

 

An Haifi Maulanmu Modibbo Jobbo A Garin Dukku Dake Jahar Gombe, An Haifeshi A Tsakanin Shekara (1895) Kokuma (1898) Inda Ya Rayu Tsawon Shekaru 78 Kokuma (81) Domin Yayi Wafati A Shekara Ta (1973).

 

{RAYUWAR SA}

 

Shehu Modibbo Ya Rayu Chikin Tarbiyya Ta Ƙwarai Wanda Ya Gajeta A Wajen Mahaifansa Wato {Modibbo Abdullahi} Da Kuma {Sayyada Fadimatu} Wato Mahaifiyar Sa.

 

Shehu Ya’ Fa’ra Karatun Addini A Gaban Mahaifansa, Yayi Karatun Al-ƙur’ani A Makarantar Mahaifinsa Sannan Kuma Ya Fara Da Kararun Littatafai A Wajen Mahaifin Sa.

 

Daga Nan Sai Shehi Ya Chigaba Da Zama A Wajan Wan Mahaifinsa, Wato Sarkin Dukku Na Wanchan Lokacin {Sarki Haruna Rashid} Ya Koma Hannun Wan Mahaifinsa Ne Kasanche War An Tura Mahaifinsa Zuwa Wani Babban Yanki Domin Ya Chigaba Da Karantar Da Al’ummar Wajen Addinin Allah S.w.t. Kamar Yadda Suka Gada (Karantarwa)

 

Modibbo Ya Zauna A Dukku Baibi Mahaifinsa Ba, Domin Kuwa Sarki Haruna Rashidi Yache “Yana Son Zama Dashi” Sirrin Hakan Kuwa Shine: Watarana Anyi Wani Bakon Babban Malam Da Hanya Ta Biyo Dashi Garin Ya’zo Wuche Wa, Ya Nuna Shehu Yache “Wannan Yaro Zai Taka Matsayi Mai Girma A Wulaya”

 

Daga Zaman Modibbo Jobbo A Garin Dukku Kuma, Sai Ya Nausa Garin Gombe Wajen Wani Babban Malami Kuma Alkalin Gari Sannan Kuma Wazirin Gari Wato {Shehu Ahmad Tijjani bn Abubakar} Wanda Maulanmu Sheikhul Islam Alhaji Ibrahim Inyass R.t.a. Yake Yabonsa A Rihla Hijaziyyah.

 

Shehu Modibbo Yayi Karatu Tukuru Inda Har Yakai Matsayinda Babu Kamar Sa Aduk Abokan Karatunsa Wanda Har Malamin Sa Dakansa Yake Chewa “Duk Wanda Yayi Karatu A Wajena, To Ya Maimaita A Wajen Modibbo Jobbo” Wanda Kuma Sau Da Yawa Yakan Fada Musu “Kudinga Daukan Karatu A Wajensa” {Modibbo Jobbo}

 

An Fada Chewa, Irin Wannan Makaranta Ta Waziri Tijjani A Wanchan Lokachin, Babu Inda Ake Samun Kamarta A Kasar Nan, Sai Kaje Garin Kano Ko Kuma Birnin Zariya.

 

{KADAN DAGA CHIKIN DALIBAN MAKARANTAR}

 

*Modibbo Jailani Yola*

*Modibbo Umar Jarkasa*

*Modibbo Tukur Gombe*

*Modibbo Muhammad Kagadama* {Jigawa

*Shehu Manzo Gombe*

*Modibbo Ali Gombejo*

 

👆Da Sauransu👆

 

Akwai Manyan Malamai Sama Da Malamai Dari Uku 300 Da Sukayi Karatu A Wannan Makaranta, Wanda Wasu Sun Fito Ne Daga Kasashe Kamar Irinsu Nigeria, Nijar, Kamaru, Central Africa Da Sauran Su.

 

{BAYAN WAFATIN WAZIRI TIJJANI}

 

Waziri Tijjani Yayi Wafati A Garin Makka Bayan Komawar Sa Aikin Hajji Inda Bayan Wafatinsa Sai Almajiransa {Waziri Tijjani} Gaba Dayansu Suka Dawo Wajen Modibbo Jobbo Da Karatu, Inda Ya Zamto Babban Malami Kuma Jagora Ga Dukkan Almajiran Maulanmu Shehu Ibrahim Inyass R.t.a. Dake Garin Gombe Da Kewaye, Inda Zawiyyar Sa Kuma Ta Zamo Head Quarter Faila Bayan Bayyanar Faidar Shehu Ibrahim.

 

Modibbo Joɓɓo Yakai Matsayin Da Duk Wani Abunda Maulanmu Shehu Ibrahim Zai Aikowa Mutanen Gombe Daga Madinatu Kaulaha Zuwa Ga Shehunnai Da Muqaddamai Da Muridai Dake Jahar Gombe Da Kewaye, Shi Yake Aikowa Direct, Domin Akwai Alaqa Sosai Tsakanin Sa Da Shehu Ibrahim.

 

{IJAZA}

 

Modibbo Jobbo Yanada Ijazozi Daban Daban Daga Shehunai Mabanbanta Kamar Irinsu Shehinsa Shehu Waziri Tijjani,

 

*Sheikh Bn Umar Ainamali*

*Sheikh Adamu Badamagare Azare*

*Shekhul Hadith, Sheikh Isma’il Bn Ali {Makkatul Mukarram}

*Sheikhul Hadi Murtania*

*Sheikh Ibrahim Inyass (R.A).

 

{ALMAJIRAN SA}

 

Sheikh Modibbo Jobbo Yanada Almajirai Da Dama Kamar Yadda Muka Fada A Baya, Inda Kusan Dukkan Almajiran Waziri Tijjani {Malamin Sa} Almajiransane.

 

Saidai Ga Jerin Sunayen Wasu Daga Chikin Almajiransa Da Sukayi Fiche. 👇

 

*Shehu Dahiru Usman Bauchi (R.A)

*Shehu Manzo Gombe (R.A)

*Shehu Modibbo Tukur Gombe (R.A)

*Shehu Ibrahim Bogo (R.A)

*Shehu Modibbo Muhammad Ali Garuza (R.A)

*Grand Khadi Yahya Ahmad (R.A)

*Sheikh Bashir Modibbo Jobbo (R.A) {Khalifa}

*Sayyidi Habibu Modibbo Jobbo (R.A) *Modibbo Jelani Yola (R.A) Wanda Shekarun Sa Biyu A Zawiyar Modibbo jobbo)

 

{MATAN SA}

 

*Sayyada Dudu*

*Sayyada Fadimatu*

*Sayyada Aishatu*

*Sayyada Fadimatu*

 

{YA’YA’NSA}

 

Sheikh Modibbo Jobbo Yanada Ya’ya Takwas, Maza Hudu Mata Hudu.

 

{MAZA}

 

*Sheikh Bashir Modibbo Jobbo*

*Sheikh Habibu*

*Sayyidi Mustapha*

*Sayyidi Ahmad Tijjani*

 

{MATA}

 

*Sayyada Balkisu*

*Sayyada Asma’u*

*Sayyada Rukayya*

*Sayyada Rabi’atu*

 

{BAYAN WAFATINSA}

 

Khalifah Sheikh Bashir Modibbo Shine Ya Chigaba Da Khalifan Chi Game Da Kuma Jagoranci Na Zawiyyar Sa Wajen Chigaba Da Bada Ilimi, Tarbiya Ta Zahiri Da Badini Bayan Wafatinsa A Shekara Ta (1973).

 

{INDA ZAWIYAR TAKE}

 

Zawiyar Tana Nan Akan Titin Jankai, Yamma Da {Gombe Division} Gabar Da Zawiyyar Sheikh Modibbo Tukur Gombe.

 

Allah Kabamu Albarkacin Sa Da Zuri’ar Sa

 

✍️ Adamu Habibu Jobbo

📝 Muhammad Izzuddin Abubakar

Share

Back to top button