Takaitaccen Tarihin Rayuwar Sheikh Ahmadu Tijjani RA Cikamakin Waliyai Kashi Na Goma (10).

CIKAMAKIN WALIYAI (10)

 

TAFIYAR SA AIKIN HAJJI

 

Hijira tana da shekara 1186, a lokacin Shehu Ahmadu Tijjani yana da shekaru talatin da shida a duniya, sai ya ga dacewar ya tafi aikin hajji da ziyarar kakan sa sanadin samuwar halittu baki daya, shugaban mu Annabi Muhammadu SAW.

 

A hanyar sa ya sadu da Sidi Muhammad ɗan Abdurrahman Al az-hariy a garin “zawawa” na Algeria inda ya karɓi Ɗariƙar Halwatiyya Rahmaniyya daga wurin sa. Ko da ya isa tunisia, ya ziyarci waliyai da dama, daga cikin su akwai Sidi Abdussamad na Ɗarikar Halwatiyya amma shima karkashin Babban Ƙudubin Kasar yake, shi kuma babban ƙudubin babu mai ganin sa sai wasu mutane hudu kuma a daren Litinin da Juma’a kawai suke haduwa dashi, daga cikin su akwai Sidi Abdussamad, Don haka sai Shehu Tijjani ya ba shi ƙwandalar zinari da ake kira “Mahbub” ya kaiwa wannan ƙuɗubin a matsayin hadiyya, ai kuwa sai ya dawo masa da amsa mai dadi daga ƙudubin cewa “Almahbub ba’athal Mahbub” wato masoyi abin ƙauna ya bada kyautar ƙwandalar zinari.

 

A tunisia Shehu Tijjani RTA ya sadu da Annabi SAW yace masa ya roki ilimin da yake so ko wani abu daban shi kuma zai ce masa Amin, Shehu Tijjani ya roƙa, sai Annabi SAW ya karanta Suratut duha, yana zuwa ayar “wala saufa” sai ya kalli Shehu Tijjani kallon soyayya sannan ya ƙarasa karatun. Shekarar Shehu Tijjani guda tsakanin garin tunis da sousse yana ibada da koyar da ilimomi har da Al-hikamil Aɗa’iyya, saboda ilimin sa ne ma Sarkin tunisia ya aiko masa sako akan yana so ya zauna a ƙasar a matsayin malamin ilimi da fatawa, zai bashi gida da albashi har da shaidar kasancewa farfesa daga jami’ar Zaituna na Tunis. Shehu Tijjani bai ce komai ba sai washegari kawai ya nemi jirgin ruwa ya tafi alƙahira (cairo) na ƙasar masar (Egypt).

 

A cairo ya sadu da Sidi Mahamudul Kurdiy RTA, yace masa “Allah yana son ka a duniya da lahira”, Shehu Tijjani yace taya kasan haka? Mahamudul Kurdiy yace Allah ne ya gaya min, sai Shehu Tijjani yace masa nayi mafarki da kai yayin da nake tunis, nace maka an yi nine da ƙarfe, sai kace kwarai haka ne, amma zaka mayar da ƙarfen nawa zuwa zinari, yana gama fadi sai Mahamudul Kurdiy yace kwarai haka yake kamar yadda ka gani. Bayan yan kwanaki sai Mahamudul Kurdiy ya tambayi Shehu Tijjani RTA game da burin sa, sai yace ni burina in samu ƙuɗubaniyyatil Uzma, Mahamudul Kurdiy yace Allah yayi maka tanadin muƙami fiye da na Imamu Shazali (wato fiye da ƙuɗubaniyyatil Uzma da yake nema).

 

Shehu Tijjani ya hau jirgi daga Misra zuwa Sa’udiyya ya ƙarasa birnin Makka a watan shawwal, hijira tana da shekara 1187.

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button