Takaitaccen Tarihin Sheikh Abdul Razak Kusa (Majnunu Barhama) Babban Malamin Addinin Islama.

TARIHIN SHEIKH ABULRAZAQI KUSA (MAJNUNU BARHAMA)

 

Daga Salihu A Adam

 

Ya rayu tsawon shekaru 75 a duniya, an haifi Shehu Abdulrazaqi Kusa a shekarar 1932, da rasuwar sa yau shekara 12 kenan. Ya rasu a shekarar 2007.

 

Shi ne dan Shiekh Muhammadu Mallumi dan Muhammadu Mai rubutu, mahaifiyar sa kuma Sayyada Aisha. An haifeshi a wani ƙauye mai suna ” Garin Malam” a cikin garin Damagaram a Jamhuriyar Niger.

 

Ya tashi a hannun kakansa bayan da Mahaifin sa ya yi hijra zuwa “ZARMO”. Yana da Shekara 6 baban sa ya tafi da shi gun mahaifinsa inda ya zauna da shi tsawon shekara biyu.

 

FANNIN KARATUTTUKAN SA.

 

Ya yi karatu a wurare da dama, ya samu haddar kur’ani yana da kananun shekaru, daga nan kuma ya cigaba da neman sauran fannonin ilimi a wurin Malamai a garuruwa daban-daban inda ya ziyarci garuruwa kamar su:- Majema, Damagaran, Mara, Madawa. Ya kuma shigo Nijeriya, ya zo unguwar Yakasai dake jihar Kano, gun Sheikh Muhammadul Muttaqah, ya je Gusau, Zaria, Nguru, Katsina, Gaidam, Yunusari, Maiduguri, Ilorin, Okene, duk dan neman Ilimin ya je.

 

Daga Shehunnan sa akwai;- Sheikh Hussain, Mal Auwal, Mal Sulaiman Damagaran, Shiekh Mal Tijjani Usman Zangon Bare-Bari shi ne ya Jazabantar da shi a Shehu Ibrahim {R.T.A.} kuma ya hadashi da Sahibil Wakati.

 

Mal Janaidu (kawun sa) shine ya bashi Dariqar Tijjaniyya, shi kuma Sheikh Sa’id As-Sanagaliy ya bashi, tarbiyyatul Azkar, Shiekh Sulaiman Damagaran kuma shine yace masa ya koma gun Sheikh Mal Tijjani Usman Zangon Bare bari.

 

Shehu ya samu Ijazoji da dama a wurin Shehinai kamar su:- Shiekh Abul Fatahi, Shiekh Sharif Ibrahim Sale, Shiekh Tijjani Inyas, Shiekh Mal Salisu ruwantsa, Shiekh Aminu Bakin Kura Bauchi. Amma mashahuriyar wanda Sheikh Ibrahim Inyass R.A. Ya bashi ita.

 

Shehu Naziru Inyass yace:- Shehu Al Qusayu shugaba ne na dukkan masoya Sheikh Ibrahim Inyass R.A.

 

Ya auri Sayyada Hafsa ɗiyar Shehu Ibrahim Inyass R.A.

 

Bayan duk Ilimin daya samu ya dawo gida Nigar ya koyar da su ga dalibai babu wani fanni a ilimi da Shehu baiyi nitso a ciki ba, dan haka Malaman Nigar suka sallama masa.

 

Shehu ya zauna a ” GAIDAMUN ” Inda ya cigaba da bad ilimi ga Jama’a safe,rana da dare.

 

Shehu ya koma “QUSA” da zama a shekarar 1984. Shine ya fara gini da zama agun, gashi yau ta zama birni, ya gina cibiyar Ilimi da Masallaci babba.

 

Shehu ya bada rayuwar shi wajen cigaban addinin musulunci da kuma yaduwar Faidha.

 

Ya rasu yabar ‘ya’ya 25, maza 12, mata 15. Ya kuma bar dubban Muridai a Jamhuriyar Niger da Nigeria da sauran qasashe da dama.

 

An rufe shi a Madinatu Qusa a shekarar 2007.

 

Khalifan sa shi ne Sheikh MAHI ABDUL RAZAQI.

 

ALLAH YA JADDADA MASA RAHMA. Amiiiin Yaa ALLAH

Share

Back to top button