Takaitaccen Tarihin Sheikh Ahmad Tijjani RA Shugaban Waliyai Kashi Na Goma Sha Hudu 14.

CIKAMAKIN WALIYAI (14)

 

ZAWIYYAR FARKO A TIJJANIYYA

 

Shekara daya bayan Annabi SAW ya cika masa komai na Ɗarikar Tijjaniyya wato shekarar 1201H kenan, a lokacin da ya ziyarci Aini Madhi sai wasu mutane su goma suka zo masa ziyara daga garin “Oud Suf”, tara daga cikin su mutanen kauyen Kamar/Guemar ne, cikon na goman su kuma daga kauyen Tagzut yake. Sun taho ƙarƙashin jagorancin Sidi Muhammad Sassi wanda ya karbi Ɗarika 1198H daga hannun Shehu Tijjani RTA.

 

Shehu Tijjani yayi musu izinin gina Zawiyya a Guemar, da suka koma sai suka samu wuri mai kyau a Tagzut suka gina zawiyyar, bayan shekara daya suka dawo wurin Shehu Tijjani yace kun gina zawiyyar? Suka ce Eh mun gina a Tagzut saboda duk wuri daya ne da Guemar din (wato babu nisa), Shehu Tijjani yace Allah da Manzon sa ba zasu karɓi Ginin zawiyya a ko ina ba sai a gabashin Guemar, don haka suka koma suka sake ginawa a Guemar, wannan shine zawiyyar farko a tarihin kafuwar Tijjaniyya.

 

MATA DA YA’YAN SA

 

A garin Abu Samguna aka haifi wata baiwa mai cikakken hankali da tarbiya kuma salihar mace wacce ake kira Sayyida Mabaruka, itace ta haifawa Shehu Tijjani RTA Ɗan sa Muhammadul Kabir wanda shima aka haife shi a Abu Samguna bayan ya ƴanta ta.

 

Matar sa ta biyu kuwa itama waliyiyar mace ce kyakkyawar gaske a hali da suffa, mai cikakken hankali da tarbiyya, sunan ta Sayyida Mubarakah, ita kuma an ce Shehu Tijjani ya same ta ne a wuraren Sudan, wasu ma suna hasashen yar nigeria ce daga Daular El-kanemi, Itama baiwa ce, Shehu Tijjani ya yanta ta kana ya aure ta.

 

Shehu Tijjani RTA yana matukar kaunar su saboda darajar su wurin Allah, har yana cewa “Albarkar Allah ta cigaba da tabbata a gidan da Mabaruka da Mubaraka suke ciki”.

 

Yayan Shehu Tijjani guda biyu sun rasu a Abu Samguna, Sidi Isma’il da Sidi Muktar, sannan a Fas kuma daya ya rasu wato Sidi Khalifa (Allah ya kara musu yarda).

 

Shehu Tijjani ya bar ya’ya biyu a duniya, Sidi Muhammadul Kabir wanda aka haifa a Abu Samguna da Sidi Muhammadus Sagir wanda ake kira da Muhammadul Habib, shi kuma a Fas aka haife shi hijira tana da Shekara 1215.

 

Sidi Muhammadul Kabir yayi shahada lokacin yakin su da Turkawa, babu wanda yasan inda kabarin sa yake, wasu sun ce ma turkawan sun yanke kansa ne suka wuce dashi gidan tarihi a Turkiyya. Duk zuri’ar Shehu Ahmadu Tijjani sun samu ne ta tsatson Sidi Muhammadul Habib kuma raudar shi tana Aini Madhi.

 

Allah ya ƙara musu yarda. Amiiiin Yaa ALLAH

 

✍️ Sidi Sadauki

Share

Back to top button