Takaitaccen Tarihin Sheikh Modibbo Aliyu Jobbo Dan Modibbo Abbdullahi (Shetiman Dukku) Dake Garin Gombe.

TAKAITACCEN TARIHIN MAULANMU SHEIKH MODIBBO ALIYU JOBBO GOMBE ALLAH YA ƘARA YARDA A GARE SHI.

 

Na samu wannan rubutun daga zuriyarsa mai albarka kuma su ne su kai izinin da a ƙara yaɗawa ƴan uwa domin mu ƙara amfana da ƙasaitaciyar rayuwar Maulana Sheikh Madibo Aliyu Jobbo.

 

Sunansa Modibbo Aliyu Jobbo ɗan Modibbo Abbdullahi (Shetiman Dukku) ɗan Modibbo Ardo Haruna jikan Modibbo Ardo Sambo Bodejo Sarkin Fulani na farko a kasar Dukku.

 

Sun zo ƙasar Dukku tun kafin jihadin Shehu Usman dan Fodiyo a shekarar ta 1804, kamar yadda ya zo a tarihi sun zo ne daga yammaci kasar Sudan wato yankin Kurdufan yankin yana maƙotaka da ƙasar Tchadi, sun biyo ta yankin Kanem Borno sun tsaya a Ƙatar kalam Dukku a yanzu wasun su kuma suka wuce garin Mama’are, wasu kuma garin Shira duk a jihadin garin Bauchi wasu kuma sun wuce yankin Jahun na jahar Jigawa.

 

An haifi Maulana Modibbo Jobbo a garin Dukku na jihar Gombe a yanzu a shekarar 1895 ko 1898 wanda tai daidai da 1315 ko da 1316 Hijiriyya….

 

Ya ta so cikin kullawar mahaifinsa Modibbo Abdullahi Allah ya ƙara yarda a gare shi, wanda ya kasance shi ma shahararren waliyin ne. Sunan mahaifiyarsa Sayyada Fadima. Ya fara karatun Alkur’ani mai girma a wajen mahaifansa ya fara karatun Ilimomin addinin musulunci duka a wajen mahaifinsa kamar irin su Fikihu, Luga, da Nahawu.

 

Ya cigaba da zama a gaban yayan mahaifinsa a lokacin shi ne sarkin Dukku na ana kiran sa da suna Sarki Haruna Rashid, mai rubutun tarihin ya ci gaba da cewa Sarki ya tura mahaifin Maulana zuwa wani yanki don ya ci gaba da gudanar da karantarwar addinin musulunci kamar yadda suka gada iyaye da Kakani.

 

Maulana ya ci gaba da zama a garin Dukku, bai bi mahaifinsa ba sakamakon Sarki Haruna Rashidi ya ce yana son zama da Maulana saboda kiyaye faɗin wani baƙon Malami da ya zo wucewa ta ƙasar Dukku ya ke cewa “Wannan matashin zai taka matsayi mai girma awilaya.

 

Maulana Modibbo Aliyu Jobbo ya shiga garin Gombe, wajen shahararren malami Alkalin gari Wazirin gari Shehu Ahmad Tijjani Ibn Abubakar

wanda Shehu Ibrahim ya ke yabonsa a cikin Rihla Hijaziyya.

 

Maulana har sai da ya kai matsayin dukkan babu kamarsa Shehin yana cewa “Duk wanda ya yi karatu a wurina to ya maimaita a wajen Modibbo Jobbo” Sauda dama ya kan ce musu Ku dinga daukan karatu a wajensa.

 

Sannan ana cewa faɗin girman shaharar wannan makaranta ta Waziri Tijjani ta kai ba’a inda ake samun irin ta sai Irin ƙasar Kano, da ƙasar Zazzau a faɗin ƙasar Najeriya ta yanzu.

 

Makarantar ta fitar da shahararun waliyi irin su.

 

Modibbo Jailani Yola

Modibbo Umar Jarkasa

Modibbo Tukur Gombe

Modibbo Muhammadu Kagadama Jigawa Shehu Manzon Gombe

Modibbo Ali Gombejo

 

Da akwai da yawansu.

 

Mai rubutun tarihin Allah ya saka masa da mafificin alheri, ya cigaba da kawo tarihin ya rubuta cewa: Waɗanda su kayi karatu suka zama manyan Malamai sunfi mutum ɗari Uku (300) daga wurare daban-daban a cikin ƙasar Najeriya, Jamhuriyar Nijar, Kamaru Jamhuriyar Tsakiyar Afirka (Central Afrika) da sauransu.

 

Bayan komawa Sheikh Waziri Tijjani Allah ya ƙara yarda a gare shi, zuwa rahmar Ubangiji a garin Makka, bayan komawarsa aikin Hajji. almajiran Shehi gaba ɗayan su sun dawo zawiyyar Maulana Modibbo Jobbo, ya zamanto malami kuma jagora ga dukkan almajiran Shehu Ibrahim Niasee, Allah ya ƙara yarda a gare shi, na kasar Gombe da kewaye kuma zawiyyarsa ta zamo cibiyar Faira bayan bayyanar Faira, domin dukkan abin da Shehu Ibrahim Niasee Allah ya ƙara yarda a gare shi, zai aiko daga Kaulaha zuwa ga mukaddamai da muridai na al’ummar ƙasar Gombe da kewaye shi ya ke aikowa ya sannan ya tara muƙaddamai ya faɗa musu.

 

Akwai alaƙa mai karfi tsakaninsa da Shehu Ibrahim Niasee Allah ya ƙara yarda a gare shi .

 

Modibbo Jobbo yana da Ijazozi daban daban daga Shehunai mabanbanta kamar su Shehinsa Shehu Waziri Tijjani, Sheikh Ibn Umar Ainamali, Sheikh Adamu Badamagare Azare, Shekhul Hadis Sheikh Isma’il Ibn Ali daga Makkatul Mukarram, Shehul Hadi Murtaniya, da kuma shakundum wato Shehul Islam Alhaji Ibrahim Niasee Allah ya ƙara yarda a gare shi.

 

Maulana Modibbo Jobbo yana da tarin almajirai da dama kamar yadda ya gabata a baya kusan dukkan almajiran Sheikh Waziri Tijjani almajiransa ne.

 

Akwai daga fitattun almajiransa akwai:

 

Maulana Shehu Dahiru Usman Bauchi

 

Maulana Shehu Manzo Gombe.

 

Maulana Modibbo Tukur Gombe

 

Maulana Shehu Ibrahim Bogo

 

Maulana Modibbo Muhammad Ali Garuza

 

Shugaban alƙalai Yahya Ahmad (Grand Khadi)

 

Maulana Halifa Sheikh Bashir Modibbo Jobbo

Sheikh Habibu Modibbo Jobbo

 

Maulana Sheikh Modibbo jelani Yola

 

Maulana Modibbo Jobbo yana da ƴaƴa masu albarka kamar haka:

 

Halifa Sheikh Bashir Modibbo Jobbo, Sheikh Habibu, Sheikh Mustafa , Sheikh Ahmad Tijjani akwai Sayyada Balkisu, Sayyada Asma’u, Sayyada Rukayya da Sayyada Rabi’atu

 

Ya koma zuwa rahmar Ubangiji a shekarar 1973 wanda ya ci gaba jagorancin almajirai da ƴaya shi ne Halifa Sheikh Bashir Modibbo.

 

Zawiyyar tana kan Titin Jankai Dawaki ta yamma a birnin Gombe.

 

Na samu rubutun daga zuriyar Maulana na ƙara wasu batutuwan kadan a rubutun saboda na shigar da shi cikin jerin waɗanda nake kilacewa.

 

Godiya ta musamman ga Adamu Habibu Jobbo Allah ya saka masa da mafificin alheri. Amiiiin

 

Daga: Mujaheed M Muh’d

Share

Back to top button