Tarihin Garin Attagazuty Da Sheikh Usman Kusfa Zaria Ya Ambata
Ina Masu Inkarin Sunan Attagazuty Da Sheik Usman Kusfa Ya Ambata?
Daga Sayyida Rahma Abdulmajid
BIRNIN TAGHAZOUT: Wani dan karamin kauyen kamun kifi ne dake da tazaran Kilo mita 19 daga garin Agadir na kudu maso yammacin Kasar Moroco, gari ne mai ban sha’awa dake bakin tekun Atlantika kewaye da tsaunukan Atlas da gandun dazuzzuka cike da bishiyoyi masu ban sha’awa.
Mutanen wannan gari sun shahara da al’adun gargajiyar Africa da na larabawa da suka hada da tsantsar karamci, bayar da abinci, da gine-ginen dauri.
Dausayin da ke cunkushe a Taghazout ya sanya garin zama kirjin biki wajen yawon shakatawa ga masu son shiga wata duniyar da har yau ba a gurbata ta daga Halittar azaliyarta ba. Ba a sare mata dazuka ba balle ta sami dumamar yanayi ko gurgusowar hamada. A gefen teku take ba a Dam ba balle wani ya toshe mata ruwa, ba a ragargaza tsaunikanta an yi tituna ba. Mutanenta zuwa ake musu ziyara ba yawo suke suna kwasar bakin al’adu ba.
Abubuwan da bakin Taghazout kan je gani sun hada da bikin hawa igiyar ruwa, Panorama, Taghazout Bay, Aljanna Valley, Sukuwan doki da sukuwar ruwa.
Mu kuma da muke daga Nesa zamu rika tuna Garin ne da Kifin gwangwani na Sadin, domin Taghazout ba baya ba wajen kamun kifayen da ake durawa a gwana-gwanai ana kawowa Najeriya.
Wani karin abin Tunawa da garin na Taghazout shine Shehu Ahmad Attalily Attagazuty, wanda karshen sunan da ke baku dariya na nufin Mutumin Taghazout.
Ban ga laifin Masu dariyar ba, amma na rasa dalilin da ya sanya Malamin ya dauki kiran sunan a matsayin wani karatu da ake neman a maimaita kuma a iya, Ko da yake ta yiwu ban kalli clip din duka bane.
Amma yaya kake ji Balarabe zai ji idan aka ce Ahmad Accediyangurasawy?