TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA ASHIRIN (20)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 20

 

HIJIRAN ANNABI (SAW) DAGA MAKKA ZUWA MADINA (Tafiyarsa zuwa Madina)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Annabi Muhammad (SAW) da Sayyidina Abubakar sun zauna a Kogon ‘Saur’ na tsawon kwanaki 3 domin bincike da Kafiren Makka keyi akansu ya tsagaita. Bayan nan sai Dan jagoransu wato Abdullahi Dan Uraiqidil-Laisi ya kawo musu ababen hawansu, sai suka cigaba da tafiya har suka isa Quba’.

 

Sun isa Quba’a ne ranar 20 ga watan Rabi’il-Auwal, bayan Aiken Annabin Rahama (SAW) da Shekara 13, Lokacin Annabi Muhammad (SAW) yanada Shekaru 53 a rayuwarsa na Duniya. Sunyi zango A Quba’ na wasu kwanaki inda Annabi Muhammad (SAW) ya Gina Masallaci.

 

Masallacin Quba’ shine Masallaci na Farko a tarihin Musulunci da Annabi Muhammad (SAW) ya Assasa ( ya Gina) da kansa, bayan sun cigaba da tafiya sai suka haɗu da Jama’a masu yawa da sukazo tariyar Annabi Muhammad (SAW) daga Madina, anan suka hadu sukayi sallar Juma’a. Wanda itace Sallar Juma’a ta Farko a tarihin Addinin Musulunci bayan hijirasa (SAW).

 

Allah ya Kara daukaka Addinin Musulunci da Musulmai. Allah ya bamu ikon koyi da Annabin Rahama (SAW). Amin

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Back to top button