TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA ASHIRIN DA BAKWAI (27)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 27

 

YAƘIN BUDE MAKKAH (Fathu Makkah)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Cikin Shekara ta 8 bayan Hijiran Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina, Kafiren Makka suka janye Kan sharudan Sulhu Hudaibiyyah. janyewarsu keda wuya, sai karfin Musulmai ya karu.

 

Annabi Muhammad (SAW) ya tinkaro Garin Makka da Kimanin Mayaka Dubu Goma 10,000. Yayinda labari ya isawa Kafiren, sukaga Bazasu iya yaƙi da Musulmai ba saboda yawansu, dayawa daga cikinsu sai suka Musulunta cikinsu harda Sarkin Makkah na wannan lokacin wato Abu-Safiyanu.

 

Cikin Zikiri Sahabbai suka Shiga Garin Makka bayan Anyi Shela an sanarda Mutanen Makka cewa duk wanda yashiga Gidan Abu-Safiyanu ya tsira, duk Wanda yashiga Gidansa baiyi niyyan fada ko yaƙar musulmai ba shima yatsira, Amma duk Wanda yafito da Niyyan yayi faɗa ko tawaye ga Musulmai to a bakin ransa.

 

Yayinda Annabi Muhammad (SAW) ya shiga garin Makka sai yayi Dawafi sannan ya Shiga Dakin Ka’abah ya Rusa Dukkanin abubuwan bautarsu da Gumakan da Kafiren Makka ke bautawa (wato gumaka 360 dinnan da suke dakin Ka’bah), Sai sahabban Annabi Muhammad (SAW) Suma sukayi Dawafi akayi ta Shela acikin Makka cewa ‘Gaskiya ta bayyana, Karya ta gushe. (Ja’al haq wa Zahaqal Baɗil)

 

Daga wannan Lokacin yazama Musulunci ya tsaya da kafafunsa, Musulmai a Garin Makka da Madina da Sauran garuruwa suna Addinin su cikin daular Larabawa cikin kwanciyar hankali.

 

Allah ya kara wa Addinin Musulunci Da Musulmai nasara, Allah ya kara mana istiqama da yaqini cikin janibin Annabi Muhammad (SAW) Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button