TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA ASHIRIN DA BIYAR (25)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 25

 

YAƘIN KHANDAQ (Yakin Gwalalo)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Yaƙin khandaq na daga cikin yaƙuna da Annabi Muhammad (SAW) yaje, yafaru ne shekara 5 bayan Hijiran Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina.

 

Wannan Yaƙin Kafurai sun shiryashi ne domin su murkushe Musulmai Baki daya suga bayan Musulunci lokaci guda. Kafiren Makka da hadin bakin Yahudawa ne suka yanke wannan shawari cewa zasu Shiga garin Madina batare da Musulmai sun Shirya ba, sukai musu farmaki su kashesu Baki daya.

 

Kimanin Mutum dubu Goma 10,000 ne adadin mayakan da Kafurai suka Tara, karkashin Jagoranci da Shugabancin Abu-Safiyanu, inda a bangaren Musulmai kuma ko rabin hakan basukai ba.

 

Dajin labari cewa Kafurai suna zuwa Garin Madina, hankalin Sahabbai ya tashi domin Jin yawan Adadin mayakan Kafiren da kuma Rashin shiri da suke ciki. Annabi Muhammad (SAW) yakira Sahabbansa domin suyi shawari, sai Salmanul-Farisi ya bada shawari da atona Rami Mai zurfi, a kewaye Madina ta yadda abokan gaba bazasu samu damar Shiga garin ba, sai aka dauki shawarinsa.

 

Nan take akayi gangami domin fita wajen gari a tona Rami a kewaye garin Madina kaman Yadda Salmanul Farisi ya bada shawari. Gamawarsu keda wuya, sai rundunar Kafurai suka iso, sai suka Kasa Shiga Madina, akayi musayen kibiya tsakanin Musulmi da kafirai, Kafurai suka koma baya.

 

Kafiren sun Kara Dawowa abun Bai yiwu ba, har sai da sukayi shigan bazata nan ma basuyi nasara akan Musulmai ba. A karshe Allah ya aikowa Kafurai wata Iska ta zame musu bala’i, sai suka gudu suka koma gida. Da ganin janyewar Kafurai, sai Musulmai ma suka koma Madina.

 

Allah ya daukaka Addinin Musulunci da Musulmai ya Kaskanta Kafurci da Kafurai Albarkan Annabi Muhammad (SAW). Amin

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button