TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA ASHIRIN DA BIYU (22)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 22

 

SHIRI DOMIN YAQI NA FARKO A ADDININ MUSULUNCI.

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Annabi Muhammad (SAW) yayi shekara 13 Yana Kiran Al’ummah zuwa ga Allah, duk da cutarwa mai tsanani da ake masa da Sahabbansa, Allah bai yimasa izini yayi yaqi ba, sai da Annabi Muhammad (SAW) yayi Hijira zuwa Madina.

 

Wannan Izini yabiyo bayan ganin yadda Addinin Musulunci yasamu karbuwa matuka wajen Al’ummah, Amma Manya daga Kafiren Makka da Madina sunyi dafifi domin ganin sun dakatar da Addinin Allah. Wanda Allah (SWT) bazai bar haka yafaru ba har sai ya cika haskensa.

 

Kafiren Makka sunyi Mamaki kwarai dagaske domin ganin yadda suke da yawa, Musulmai kuma ƴan Kadan, suna ganin yadda sukeda Kudi da guzuri, Musulmai kuma Basuda komai, Amma sunada Allah (SWT). Kuma suna ganin ƴan uwantaka na dangi, yare da Ƙabila dake tsakaninsu, Abun kunya ne ace Larabawa musamman Quraishawa suna Yaqin junansu.

 

Domin ganin an karya Kafiren, an nemi Kai musu Hari domin raunata harkan kasuwancinsu ne Wanda hakan shine yayi sanadiyar yakin Farko wato Yakin Badar Babba.

 

Annabi Muhammad (SAW) ya halarci yaƙi guda 27 dakansa, daga ciki harda; Yakin Badar Babba, Yakin Uhdu, Hudaibiyyah, Fathu Makkah, Hunain da sauransu. yaƙoƙin da Annabi Muhammad (SAW) yayi wakilci amma baije dakansa ba 47. zanyi bayanin kaɗan daga cikin yaƙoƙin da Annabi Muhammad (SAW) yaje dakansa daga rubutu na na gobe Inshallah.

 

Allah ya daukaka Addinin Musulunci da Musulmai, a duk inda suke, Allah ya Kaskanta Kafurci da Kafurai a duk inda suke, Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button