TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA ASHIRIN DA DAYA (21)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 21

 

HIJIRAN ANNABI (SAW) DAGA MAKKA ZUWA MADINA (isar Annabi (SAW) garin Madina)

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Da isar Annabi Muhammad (SAW) garin Madina Ansar (Musulman Madina) suka kewayeshi suna Murna suna masa Maraba da zuwa garinsu (Madina), suna rera masa wannan Sananniyar wakar ‘Ɗala’al Badru Alaina…’.(Zan kawo Kasidar in Fassarata bayan na gama tahirin Inshallah)

 

Kowa naso Annabi Muhammad (SAW) ya sauka a gidansa, Amma Annabi Muhammad (SAW) yayi musu ishara cewa zai Gina Masallaci da gidansa Amma a duk inda Taguwarsa tayi zango cikin Garin Madina. Bada jimawaba, bayan sake Linzamin taguwar Annabi Muhammad (SAW), sai tayi zango a gefen Gidan Abu-Ayuba Al-Ansari.

 

A Gidan Abu-Ayuba Al-Ansari Annabi Muhammad (SAW) ya zauna kafin a Gama gina Masallaci da gidansa. Aikin gayya akayi tsakanin Muhajirun (Wadanda sukayi hijira daga Makka zuwa Madina) da Ansar (Musulman Madina). Annabi Muhammad (SAW) dakanshi ba’a barshi a baya wajen wannan aikin ba.

 

Mafi yawancin Sahabbai sun dawo Madina, wadanda suka rage a Makka saidai Nakasassu, ko wadanda aka dauresu ko aka Kullesu. Nan take aka Kafa Ƙasa da Daular Musulunci a Madina inda Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa suke zaune cikin Aminci.

 

Ganin haka yasa Yahudawan Madina suka Fara bayyana Gaba, Fushi da Hassada ga Musulmai da Musulunci. Annabi Muhammad (SAW) ya kulla Alqawari dasu cewa kowa bazai cutar da kowa ba, kuma kowa zaiyi Addininsa cikin Aminci. Yahudawan Madina sune; Banu Nathir, Banu Qainuqa’a, Banu Kuraiza.

 

Alhamdulillah daga wannan lokacin Nasara maigirma ta fara bayyana ga Musulmai da Addinin Musulunci, Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa suka fara samun saukin takura da matsi. Allah ya kara daukaka Addinin Musulunci. Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Back to top button