TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA ASHIRIN DA HUDU (24)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 24

 

YAƘIN UHUDU

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Yaƙin Uhudu shine Yaƙi na biyu da Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa sukayi. Anyi yaƙin ne bayan Yakin Badar da Shekara 1, (Shekara ta 3 bayan hijira). Dalilin yakin shine, Kafiren Makka sunyi shiri domin daukan fansa ga wadanda aka kashe musu a Yaƙin Badar.

 

Kafirai sun fita da Runduna Mutum dubu uku 3,000 Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa kuma Basu wuce Mutum dubu daya 1,000 ba. A hanyarsu tazuwa Filin yaki daga Madina, Munafukai Dari Uku 300 suka fita a cikin Musulmai suka koma gida karkashin Jagorancin Babban Munafukinnan wato Abdullahi Dan Ubayyu. Sai ya saura Musulmai 700. wanda zasu gwabza da kafirai 3,000.

 

Da isarsu Uhudu Mutum 50 daga Sahabban Annabi Muhammad (SAW) suka hau Kan Dutse domin tabbatar da tsaro ga Musulmai, sai Annabi Muhammad (SAW) yayi Musu izini da cewa karsu bar Kan wannan Dutsen, koda sunga ba Musulmai ne sukayi nasara ba. Daganan sai aka fara yaƙi.

 

SAHABBAI SUN MANTA DA UMARNIN ANNABI (SAW), SUN SAUKO DAGA KAN DUTSE.

 

Fara yaki keda wuya, Kafiren Makka suka Fara komawa baya, suna guduwa. Musulmai suka bisu a baya suna yakarsu, ganin haka sai Sahabbai suka dauka yaki ya kare anyi Nasara, suka Shagala da kwasan Ganima, ganin haka Wanda suke Kan Dutse suka manta da Umarnin da aka musu, suka sauko domin samun/ɗiban Ganima.

 

Saukowansu keda wuya, Ashe rundunar Khalid ɗan Walid na tabayan Dutsen, kawai sai suka kewayo da rundunarsa suka afkawa Musulmai ta baya, ganin haka sai Wandanda ke gudu daga Kafurai suka juyo, Nan take akasa Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa a tsakiya yaki ya koma sabo.

 

Basu gusheba suna fafatawa a Filin Yakin ba, har Saida aka kashe dayawa daga cikin Sahabban Annabi Muhammad (SAW), aka raunata dayawa daga cikinsu, yakasance har shima Annabi Muhammad (SAW) da kansa yaji raunuka. A karshe dai Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa kan dutse suka hau domin ganin yadda yakin ya kasance. Kafirai sunyi murna kwarai da gaske ganin yadda sunkayi nasara a yaƙin. Amma cikin ikon Allah sai hakan ya zama nasara ga Musulunci, domin duk wanda aka kashe shahada yayi, kuma Allah zai maye gurbinsa da Dubban mutane. Alhamdulillah.

 

A Wannan Yaƙin Sahabbai sama da 70 ne sukayi Shahada, daga ciki harda Baffan Annabi Muhammad (SAW) Sayyidina Hamza, a bangaren Kafurai kuma an kashe Mutum 23. Haka Yaƙin Uhudu ya kasance atakaice.

 

Allah yayi hakane domin ya koyar damu cewa wata Rana zamuyi farinciki wata Rana kuma Bakinciki, wata Rana nasara wata Rana rashinta, Allah ya Kara mana Imani da juriya ya shiryar damu Hanya Madaidaiciya. Amin

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button