TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA ASHIRIN DA SHIDA (26)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 26.

 

SULHU HUDAIBIYYAH

 

Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain

 

Wasu daga cikin Malamai suna cewa Yakin Hudaibiyyah, wannan ya farune cikin Shekara ta 6 bayan Hijiran Annabi Muhammad (SAW) daga Makka zuwa Madina.

 

Annabi Muhammad (SAW) ne yafito da Sahabbansa adadinsu kimanin Dubu daya da Dari biyar 1,500, sun fita daga Madina zuwa Makkah domin suyi aikin Umura.

 

Yayin da Kafiren Makka sukaji labarin haka, sai sukayi gangami, a Karshe sai suka nemi zasuyi sulhu da Annabi Muhammad (SAW), inda suka tura mutane daban-daban cikinsu harda Khalid Bin Walid. Amma Annabi Muhammad (SAW) bai yarda dasu ba, saida suka tura Suhailu Dan Amr tukunna, Annabi Muhammad (SAW) ya yarda da ayi sulhu dasu bisa wasu sharuda. Daga cikin Sharudan sun haɗa da;

1. Duk wanda yayi hijirah batare da izinin Iyayensa ko mai jiɓintar lamarinsa ba, za’a dawo dashi Makka, wanda yazo Makka kuma daga musulmai ba za’a barshi ya koma Madina ba.

2. Za’a tsagaita yaƙi tsakanin Musulmai da kafurai tsawon wannan lokaci.

3. Annabi Muhammad (SAW) zai juya ya koma Madina a wannan shekarar sai wata shekara ya dawo. Da sauransu.

 

Sudai Kafiren Makka abunda Sukeso shine Annabi Muhammad (SAW) karya gabatar da aikin Umura wannan Shekarar koma ta yaya ne, ya bari sai a shekara ta gaba, sai yazo yayi. Annabi Muhammad (SAW) ya amince musu akayi sulhu Akan hakan.

 

Bayan gama sulhun ne Annabi Muhammad (SAW) yayiwa Sahabbai Umarni da kowa ya yanka abun yankansa a wannan wajen, kuma su shirya domin komawa Madina. Abun bai yiwa Sahabbai da yawa daɗi ba, amma haka dai sukabi umarnin Annabi Muhammad (SAW).

 

Allah muna tawassuli da wannan Sulhu da akayi, Ka tabbatar damu cikin yimaka ɗa’a da bin koyarwan Annabi Muhammad (SAW) a kowani lokaci. Amin.

 

07032509197

yaseen9253@gmail.com

Share

Back to top button