TARIHIN MANZON ALLAH ANNABI MUHAMMADU SAW KASHI NA ASHIRIN DA TAKWAS (28)

TARIHIN ANNABI MUHAMMAD (SAW) Kashi na 28.
YAƘIN HUNAIN
Daga: Muhammad Yaseen Bin Hussain
Bayan Fathu Makkah akayi Yakin Hunain. Kabilar Saqeef da Huwazin da wasu kananan Kabilu dake goyamusu baya sune suka yanke hukunci domin su yaki Annabi Muhammad (SAW) da Musulmai kafin Da’awar Musulmai ta iso Kansu idan basuyi Imani ba, a murkushesu a yaƙesu, shine sukace bari su yaƙi musulunci kafin a yaƙesu.
Kabilun sunada Mayaka kwararru masu Dunbin yawa, suka yi gangami na musamman domin wannan yakin. Annabi Muhammad (SAW) da Mayaka Dubu Goma 10,000 ne suka taso daga Madina, daga Makka kuma Musulmai Dubu Biyu 2,000 wasu Malamai sukace 1,000 ne daga Wandanda suka Musulunta ranar Fathu Makkah.
Da isar Annabi Muhammad (SAW) da Sahabbansa wajen yaƙin (Hunain), sai aka fara musu ruwan kibiya, Ashe Kafiren sunyi kwanto a tsakanin Duwarwatsu, dama Kafiren sun riga Musulmai isa Filin yaƙin, sai suka Shirya harin bazata ga Musulmai.
Aka fafata a Fagen daga, har Saida aka danna Musulmai, suna komawa baya, har Saida ya kasance bakowa tare da Annabi Muhammad (SAW) sai Manyan Sahabbai, Annabi Muhammad (SAW) yana Kan Alfadarinsa Mai suna Dul-Dulu ya Danna cikin Kafiren Yana cewa “Tabbas Nine Annabi Tabbas Nine Dan Abdullahi Dan Abdul-Mutallib…”
Annabi Muhammad (SAW) ya durkusar da Alfadarinsa, ya Debi Kasa da hannunsa Mai Albarka ya watsawa Kafurai Makiya Allah, sai dukkan su Kasa ya shiga Idanuwansu basa gani, Sayyidina Abbas yayi Kira ga Musulmai cewa adawo Fagen daga, da yunkurowar Musulmai sai sukabi takan Kafiren da Sara da suka, aka Kashe dayawa daga cikin Kafurai aka kama Fursinonin yaki da yawa, aka samu ganiman yaki Mai yawa.
Allah ya Kara daukaka Addinin Musulunci da Musulmai ya Kaskanta Kafurci da Kafurai Albarkacin Annabi Muhammad (SAW). Amin.
07032509197
yaseen9253@gmail.com